Za mu koma Kotun Koli kan korar karar Atiku - PDP

Atiku da Secondus

Asalin hoton, TWITTER/PDP

Bayanan hoto,

PDP ta ce an zalunce ta sau da dama

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta ce za ta koma gaban Kotun Kolin kasar don ta sake nazari kan wasu hukunce-hukuncen korar kararrakin 'yan takararta a zaben kasar na bara, ciki har da na dan takarar shugaban kasarta Atiku Abubakar.

A ranar 30 ga watan Oktoban 2019 ne alkalan kotun kolin bakwai, wadanda alkalin alkalan kasar Mai shari'ah Tanko Mohammed ya jagoranta, suka kori karar da Alhaji Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP suka daukaka.

Yanzu babbar jam'iyyar adawar na cewa hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yanke kan zaben gwamna a baya-bayan nan ya sanya ta ganin bukatar sake komawa gabanta don ta warware hukuncin da ta yi na baya.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri, sakataren PDP na kasa, ya shaida wa BBC cewa an zalunci jam'iyyar ba sau da dama shi ya sa suka ga ya dace su kai wa Kotun korafinsu na son a sake nazari kan hukunce-hukuncen

"Misali zaben jihohin Kano da Kogi, kotu ta ce wadannan zabukan sun yi amma saboda an ki sa hannu kan dokar zabe, babu yadda za mu yi mu ba da hujjar cewa an yi magudi."

"Za mu fara da zaben Katsina da na Shugaban kasa, sannan idan muka gama bincikenmu sai mu ga wadanne ne kuma za mu bukaci a gyara mana", a cewar Sanata Tsauri.

Ya ce yanzu suna tattara bayanai kuma nan da dan lokaci za su sanar da sauran jihohin da za su so a sake duba hukuncinsu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sanata Tsauri ya yi tsokaci kan hukuncin zaben jihar Bayelsa da jam'iyyar APC mai mulki ta bukaci kotun koli ta yi nazari a kai.

Kotun dai ta sauke David Lyon, na jam'iyyar APC ne , mutumin da a baya INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zabe, saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa INEC takardun bogi lokacin da ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.

Daga nan ne kuma sai jam'iyyar APC din ta shigar da bukatarta ga kotun kolin, na sake duba hukuncin sauke David Lyon.

Sanata Ibrahim Tsauri ya ce tunda har jam'iyya mai mulki ta mika wannan bukata me zai hana ita ma babbar jam'iyyar hamayya mika irinta?

"An yanke wa APC hukunci kan takarda kuma takarda babu ita. Muma an yanke mana hukunci da yawa kan rashin takardu kuma mun amince.

"Sai ga shi kuma kotun da kanta ta ce tunda takardunsa (Biobarakuma DEgi-Eremienyo) ba su yi dai-dai ba an soke zaben. To tunda kotun ta ce kuskure ne za mu je mu ce mata mu ma ga kura-kuran da muka lura da su muna so ta gyara," in ji Ibrahim Tsauri.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, jam'iyyar PDP ta ce jam'iyya mai mulki na so ta tayar da husuma da kuma lalata demokuradiyya shi ya sa ta bukaci kotun koli ta yi nazarin hukuncin na Bayelsa.

Jam'iyyar ta ce saboda yadda ta ke martaba demokuradiyya shi ya sa ta rungumi kaddara bayan da kotu da yanke hukunci kan zabukanjihohinKaduna da Katsina da Katsina da Osun.

Amma ta ce tunda hanyar da jam'iyyar APC ta dauka kenan, ita ma a shirye ta ke ta bukaci kotun kolin da ta yi bitar hukunce-hukuncen da suka kunshi takardun bogi ko kuma gabatar da bayana karya.

Ga karin labarai da za ku so karantawa: