An gano riga-kafin cutar coronavirus

Cutar Coronavirus

Asalin hoton, Science Photo Library

Rahotanni sun bayyana cewa masana kimiyya a China sun kirkiro riga kafin cutar coronavirus kuma suna fatan fara gwadawa a kan mutane.

Wata jaridar gwamnatin kasar mai suna Global Times ta ce wani farfesa a jami'ar Tianjin ya sha riga kafin sau hudu kuma ba ta yi masa wata illa ba, don haka ya yi imani cewa ana iya samar da riga kafin cikin gaggawa kuma da yawa.

Haka kuma, rahotanni sun bayyana cewa masu bincike a Amurka sun gano wani riga-kafin wanda ake gwada amfani da shi a halin yanzu.

Kwararru sun yi gargadin cewa babu tabbas kan tasirin da riga kafin zai yi har sai an yi cikakken gwaji kuma ana iya daukar watanni kafin a samar da shi a ko ina.

A baya dai, an gano cewa maganin zazzabin cizon sauro na Chloroquine phosphate wanda aka fi amfani da shi a nahiyar Afirka musamman a shekarun 1980 da 1990 yana warkar da cutar numfashi ta coronavirus.

Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar China ce ta bayyana hakan ranar Laraba.

Gidan talbijin na China Global Television Network ya ruwaito cewa daukacin masana a kasar sun amince a yi amfani da Chloroquine phosphate domin maganin cutar Covid-19 virus, wadda aka fi sani coronavirus.

Yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya kawo yanzu ya wuce dubu tamanin, yayin da annobar ke kara bazuwa.