Kalli hotunan ganawar Buhari da hafsoshin tsaron Najeriya

Hafsoshin tsaron Najeriya sun gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari, karon farko tun bayan zargin da mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro, Babagana Monguno, ya yi cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari yana yin katsalandan kan harkokin tsaron kasar.

Manjo-Janar Monguno mai ritaya ya ce katsalandan din da Abba Kyari ke yi a aikinsa ya takaita nasarorin da ake samu a kokarin inganta tsaro a Najeriya.

Babu dai wani martani daga bangaren shugaban ma'aikatan.

A cewar Monguno, a wani lokaci Abba Kyari kan yi gaban-kansa wajen jagorantar zama da hafsoshin tsaron da kuma wasu muhimman mutane irin jakadun wasu kasashe a Najeriya ba tare da sanin Shugaba Buhari ba.

'Abin da ya sa Munguno bai halarci ganawar ba'

Sai dai a ganawar da hafsoshin tsaron suka yi da Shugaba Buhari, ba a ga fuskar Manjo-Janar Monguno.

Ko da yake mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad tun farko ba ya cikin jami'an tsaron da ke ganawa da Shugaban kasar.

Hafsoshin tsaron da suka halarci ganawar su ne: Hafsan tsaron kasa, Janar Abayomi Olonisakin, Hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur .Yusuf Buratai, Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas, Hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar da kuma Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, Mr Mohammad Adamu

Asalin hoton, Instagram/@bayoomoboriowo

Asalin hoton, Instagram/@bayoomoboriowo

Asalin hoton, Instagram/@bayoomoboriowo

Asalin hoton, TWITTER/@BashirAhmaad

Asalin hoton, TWITTER/@BashirAhmaad

Asalin hoton, TWITTER/@BashirAhmaad