Shugaban Faransa ya 'ci mutuncin' shugaban Kamaru

Biya da Macron

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Macron ya ce Paul biya yana matukar taka hakkin dan adam

Matasa da dama ne suka yi zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke Yaoundé, babban birnin Kamaru, saboda kalaman "muzantawa" da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kan Shugaba Paul Biya.

Hakan ya faru ne bayan wani bidiyo da ya watsu a shafukan sada zumunta a karshen mako ya nuna Shugaba Macron yana shaida wa wani mai fafutuka dan kasar a Paris cewa ya matsa lamba kan Mr Biya domin sako shugaban 'yan hamayyar kasar Maurice Kamto - wanda aka sako shi daga kurkuku wata tara bayan an kama shi a watan Oktoba na 2019.

A cikin bidiyon, an ji Shugaba Macron yana cewa "akwai hakkokin dan adam" da ake takawa fiye da misali a kasar Kamaru - ya yi kalaman ne kwanaki kadan bayan 'yan bindiga sanye da kakin soji sun kashe mutum 22 a kauyen Ngarbuh da ke Arewa maso Yammacin kasar.

Mr Macron ya shaida wa mai fafutukar cewa "Zan kira Shugaba Biya makon gobe kuma zan matsa masa lamba sosai ta yadda za a kawo karshen wadannan matsaloli."

Sai dai kalaman ba su yi wa gwamnatin Kamaru dadi ba.

Wani mai zanga-zanga ya ce "Muna kaunar shugabanmu. Mutum ne mai son zaman lafiya."

"Babu wani darasi da Faransa za ta koya wa Kamaru kuma dole Macron ya nemi afuwa saboda cin mutuncin da ya yi cewa shugabanmu dan barandarsa ne," a cewar wani mai zanga-zangar.

Wani kuma ya rike kwalin da aka rubuta cewa ya kamata Macron ya rika girmama dattawa, yana mai cewa Kamaru kasa ce mai cin gashin kanta.

Mai fafutukar, Yvone Mumah Biya, ya ce gwamnatin Kamaru ce ta daukki nauyin masu zanga-zangar.

Bayanan hoto,

Wani mai zanga-zanga ya bukaci Macron ya daina raina dattawa