Mata ta 'auri' maza biyu a Kano

.

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar Hisbah da ke Kano ta tabbatar da karbar koke kan wata mata mai suna Hauwa Ali, mai shekara 30, wadda ta 'auri' maza biyu a unguwar Mariri da ke karamar hukumar Kumbotso.

Hisbah ta ce, mijin Hauwa'u na farko Bello Ibrahim ne ya kai koke hukumar bayan ya dawo daga jinyar da ya shafe tsawon lokaci yana yi a garinsu.

Bello Ibrahim, mai shekara 40, ya ce ya gamu da rashin lafiya ne wadda ta kai har sai da ya tafi gida ma'ana garinsu neman magani, to bayan shekara biyu ya warke shi ne ya dawo wurin iyalansa.

Bello ya ce "Ko da na shiga gida, sai na tarar da wani kato a kan gadon matata, sai kawai na saki ihu, a tunani na kwarto ne, to amma sai na fuskanci shi mutumin ko gezau bai yi ba da ya ganni".

Ya ce "Kawai sai na ji ya tambaye ni lafiya, ka shigo mini gidan mata?".

Bello ya ce daga nan ne sai suka fara cacar baki, da ya ga abin ba sauki shi ne ya garzaya hukumar Hisbah da ke Kumbotso ya kai kara.

Ko da Hisbah ta kira sabon mijin Hauwa'u, Bala Abdulsalam, mai shekara 35, don jin bahasi, sai ya ce shi bai san tana da aure ba, domin ce masa ta yi bazarawa ce amma tana da 'ya'ya shida.

Bala, wanda direban babbar mota ne, ya ce "Daga nan ne sai muka daidaita kan mu har ta amince da sadakin naira dubu ashirin".

Ko da Hisbah ta ji ta bakin Hauwa'u, ta shaida mata cewa sai da Bello mijinta na fari ya sake ta sannan ta sake yin aure.

Hauwa'u ta ce" Tun kafin ya kwanta rashin lafiya na ce ya sake ni, kuma ya sake ni sannan na zauna na yi idda a gidan Bello tare da 'ya'yana".

Ta ce ko bayan da Bello ya sake ta sai da ya ci alwashin ba zai mayar da ita ba.

Hauwa'u ta kuma shaida wa Hisbah cewa, sabon angon nata tsohon masoyinta ne tun tana budurwa.

To sai dai kuma Bello ya ce shi bai sake ta ba.

A nata bangaren, hukumar Hisbah ta ce, sakamakon sauraron dukkan bangarorin dole ne sai an kai ga zuwa kotu don warware matsalar.

Babban daraktan hukumar Dr Aliyu Musa ya ce za su kara yin bincike a kan wannan al'amari, sannan daga baya a gurfanar da mutanen uku gaban kuliya.