Olisa Metuh zai sha daurin shekara bakwai a gidan yari

Olisa Metuh

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Olisa Metuh ya karbi N400m daga wurin Sambo Dasuki

Wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara bakwai kan tsohon kakakin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Olisa Metuh.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan ta same shi da laifin almundahanar N400m.

Da yake yanke hukunci a yau, alkalin kotun, Mai shari'a Okon Abang, ya ce ya samu tsohon jami'in na PDP ne da laifin halatta kudin haramun.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ce ta shigar da shi kara, inda ta zarge shi da karbar kudin daga hannun tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsawo, Kanar Sambo Dasuki.

Mai shari'a Abang ya ce "Ra'ayina shi ne Metuh ya karbi N400m daga ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro ba tare da wata hujja ta kwangila ba; don haka an same shi da laifi daya na halatta kudin haramun."

Kan tuhuma ta biyu kuma da ke da nasaba da karkatar da kudin, alkalin ya ce akwai shaida cewa an yi amfani da kudin wajen gudanar da wasu ayyukan PDP.

Alkalin ya kuma kara da cewa Metuh ya yi amfani da kudin wajen sayen kadarori a Banana Island da ke Legas.

Mai shari'a Abang ya ce shaidar ta nuna cewa an wawure kudaden domin bai wa PDP dama lokacin babban zaben kasa da aka yi a 2015.

Ya kara da cewa Metuh ya gaza yin bayani kan yadda aka ciri N50 daga N400 zuwa asusun hadaka mallakin shi da mai dakinsa.

Alkalin ya ce "a don haka a bayyane take cewa wanda ake karar ya karkatar da kudin ga yakin zaben PDP kuma na same shi da laifi."

Game da tuhumar boye kudaden kuma, Mai shari'a Abang ya ce wata takardar biyan kudi ta nuna cewa an saki kudaden domin samar da tsaro amma kuma aka boye inda aka yi amfani dasu domin yakin zaben PDP da kuma bukata ta kashin kai.

Alkalin ya yanke cewa "na same shi da laifi kan tuhuma ta uku."

Ya kuma yanke hukunci kan tuhuma ta hudu game da zargin rarraba kudaden ta haramtacciyar hanya.

Asalin hoton, @officialEFCC/Twitter