Za mu fara gurfanar da iyayen almajirai a kotu - Ganduje

Gwamna Ganduje

Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA ANWAR

Bayanan hoto,

Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai tallafa wa makarantun allo amma dole ne a fara koyar da turanci da lissafi

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta haramta bara a titunan jihar.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka ranar Talata yayin bikin mika takardun daukar aikin malanta ga mutane 7,500 a birnin Kano.

Ganduje ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga 'yan firamare da sakandare a fadin jihar.

Ya ce daga yanzu dole ne makarantun allo su shigar da darussan turanci da lissafi cikin tsarin koyarwarsu.

Gwamnan ya ce "idan har kana zaton cewa ba za ka karbi tsarin nan na mu ba, to sai dai ka bar jihar."

A yayin jawabin, Ganduje ya bayyana cewa daga yanzu duk yaron da aka kama yana bara to za a kamo mahaifinsa ko mai kula da shi, kuma a gurfanar da shi gaban kotu saboda rashin mutunta dokokin

jihar.

Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA ANWAR

Bayanan hoto,

Wasu alkaluma na nuna cewa akwai fiye da yara Miliyan uku da ba sa zuwa makaranta kuma mafi yawansu a arewacin Najeriya suke

Ko a makon jiya ma sai da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatoci da su ringa kama duk wani mahaifi da aka samu dansa yana bara da sunan karatun Alkur'ani.

Matsalar bara musamman ga yara kanana na daga abinda ake dauka a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin dake addabar arewacin Najeriya.

Wasu alkaluma na nuna cewa akwai fiye da yara Miliyan uku da ba sa zuwa makaranta, kuma mafi yawansu suna yankin arewacin kasar ne.

A baya ma gwamnatoci a jihar ta Kano sun taba hana bara, sai dai matakin bai yi tasiri ba, saboda abinda wasu masana ke cewa rashin ingataccen tsari da tanadi.