Najeriya: Mabiya darikar katolika na alhinin rashin tsaro

Catholic Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A shekarar 2018, mabiya darikar Katolika sun yi maci don nuna rashin jin dadinsu bisa munanan hare-hare da ake kai wa a Najeriya

A yau ne mabiya darikar Katolika a Najeriya suka fara gudanar da azumi da kuma alhini ta hanyar sanya bakaken tufafi a fadin kasar don bayyana damuwarsu game da tabarbarewar tsaro.

Darikar Katolikan ta bukaci mabiyanta su nuna alhini a yau tare da gudanar da maci nan gaba cikin wannan mako a Abuja kan wannan matsala da ke addabar sassan Najeriya.

Babban Sakatare na darikar Katolika, Rabaran Zacharia Samjumi ya ce duk wani mai bin darikar zai sa bakaken tufafi don nuna bakin ciki dangane da kashe-kashen mutane da satar mutane don kudin fansa.

"Manyan malaman cocin Katolika a Najeriya sun yi shawarar cewa yau mu nuna bakin cikinmu," a cewarsa.

Ya ce azancin yin haka shi ne don ankarar da gwamnati ta tashi ta kare jama'ar kasar.

Mabiya darikar Katolikan za su yi tattaki ranar Lahadi a Abuja sanye da bakaken tufafin don ida nufinsu na kira ga gwamnatin Najeriya ta dau kwararan matakai don shawo kan matsalar tsaro a kasar.

Rabaran Zacharia ya ce a ganinsu gwamnati tana sake da lamuran tsaro.

"A shiga gidan mutane a kama su, ko a shiga makaranta a sace yara, ga fashi a kan hanya. Sannan 'yan Boko Haram da aka kama mun ji ana sakinsu su dawo cikin mutane," in ji Rabaran Zacharia.

Ya ce sai gwamnati ta tashi tsaye ta kawo karshen wadannan ayyuka kafin mutanen Najeriya su samu kwanciyar hankali su ci gaba da gudanar da ayyyukansu yadda ya kamata.