Mutum 20 sun mutu a rikici tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmi

Police walk past a vehicle set on fire by protesters in Delhi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rikicin ya barke ne tsakanin mabiya addinan biyu

Ana ci gaba da zama cikin fargaba a Delhi, babban birnin India bayan an kwashe dare na uku a jere ana rikici, inda rahotanni suka ce mabiya addinin Hindu sun kona gidaje da shagunan Musulmi.

Mutum ashirin sun mutu ya zuwa yanzu a rikicin da ake gani shi ne mafi muni da ya auku a babbarn birnin na india cikin shekaru aru-aru.

Ranar Lahadi ne aka yi arangama tsakanin masu zanga-zangar ke goyon baya da masu adawa da wata dokar zama dan kasar wacce ake takaddama a kanta.

Amma tuni rikicin ya rikide ya zama na addini, inda rahotanni suka ce wasu na kai wa mutanen da ke bin addinin da ba nasu ba hari.

Hotuna da bidiyo da kuma rahotanni daga shafukan sada zumunta sun nuna yadda rikicin ya kazance - inda 'yan daba suke kai hari kan mutanen da ba sa dauke da makamai, ciki har da 'yan jarida; da wasu mutane dauke da adduna da sanduna suna kewaya hanyoyi; da kuma mabiya addinin Hindu da ke kai hari kan Musulmi.

Ministan birnin Delhi Arvind Kejriwal ya bayyana rikicin a matsayin "abin tayar da hankali" sannan ya yi kira "a kawo agajin sojoji".

An fi kai hari a yankunan da Musulmi suka fi yawa - kamar su Maujpur, Mustafabad, Jaffrabad da kuma Shiv Vihar - da ke arewa mas gabashin Delhi.

Wakilin BBC Hindi Faisal Mohammed ya ce titunan yankunan cike suke da duwatsu da fasassun gilasai da ababen hawan da aka kona da kuma warin hayaki da ya turnuke.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kone akalla masallatai biyu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kone ababen hawa a birnin

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan sanda da masu zanga-zanga sun fafata a Delhi