An hana yanka jakuna a Kenya

Jakuna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An ce ana yanka jakuna kusan 1000 a kullum

Ministan harkokin noma a kasar Kenya Peter Munya, ya ce daga watan Maris 2020, za a daina yanka jakuna a mayanka a kasar.

Kasar wadda ke a Gabashin Afirka, ta halatta cinikin naman jakuna a 2012 domin gamsar da bukatun kasar China.

Ministan, ya ce an yi babban kuskure wajen daukar matakin sayar da jakunan, saboda yanzu yawansu na raguwa sosai a kasar.

Yawancin mutanen da ke yankunan karkara na amfani da jakuna wajen dibar ruwa da itace.

Ministan ya ce raguwar jakunan a kasar wata babbar barazana ce ga mata, saboda ayyuka za su yi musu yawa.

Kenya tana da jakuna kusan 600,000 idan aka kwatanta da miliyan 1 da dubu dari 8 da kasar ke da su shekaru goma da suka shude.

A ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020 ne manoma mata da maza a Kenya suka gudanar da wata zanga-zangar lumana a kofar ofishin Mista Munya da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya inda suka bukaci da a kare jakuna daga karewa.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce " Idan ana sace ko kashe jakuna, mata ne ke komawa jakunan".

Daga baya Mista Munya, ya shaida wa manema labarai cewa lasisin da aka ba wa wadanda ke aiki a mayankar kasar ta yanka jakuna zai dai na aiki daga watan Maris 2020.

Bayanan hoto,

Fatun jakuna

Ministan ya ce daga yanzu dokar yanka jakuna sannan ayi amfani da naman ko a fitar da shi zuwa wasu kasashen yanzu za ta daina aiki.

Ya ce " Amfanin da jakunan ke yi ga al'ummarmu, ya fi muhimmanci a kan yanka su a ci nama".

Yawan yanka jakunan da ake yi ya sa an samu kasuwannin bayan fagen da ke fasa kaurin fatun jakunan abin da ke janyo barayi ke satar jakunan mutane domin a yanka su siyar da fatar.

Akwai mayanka hudu a Kenya da aka ba wa lasisin yanka dabbobi.

Wata kungiya da ke fafutukar kare jakuna mai suna Brooke East Africa, ta kiyasta cewa ana yanka akalla jakuna 1000 a kullum a Kenya.

China na matukar bukatar fatun jakuna.

Suna amfani da fatun ne wajen hada abinci da kuma maganin gargajiya a kasarta China.

Wata kungiya mai kare jakuna d ake Birtaniya mai suna The Donkey Sanctuary, ta kiyasta cewa ana siyar da fatun jakuna miliyan daya da dubu dari takwas a kowacce shekara.

Adadin jakunan China ya ragu daga miliyan goma sha daya zuwa miliyan uku daga 1990 zuwa 2020 inji kididdigar kasar.

Kasashe kamar su Uganda da Tanzania da Bostwana da Nijar da Burkina Faso da Mali da kuma Senegal tuni suka haramta fitar da jakuna ko namansu zuwa China.