Kotun Koli ta yi watsi da karar APC kan zaben Bayelsa

@ Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar da jam'iyyar APC ta shigar na neman kotun ta sake nazari kan hukuncin da ta yanke na karbe nasarar 'yan takararta David Lyon da mataimakinta Degi Eremionyo a zaben gwamnan jihar Bayelsa.

APC dai ta koma Kotun Kolin ne domin neman kotun ta warware hukuncinta da ya ba wa Duoye Diri na jam'iyyar PDP nasara a jihar.

Da ta ke karanta hukuncin, Mai shari'a Amina Augie ta bayyana cewa, kotun ba za ta yi bitar hukunci da ta yanke a baya ba, saboda ba ta da hurumin sake waiyayar hukuncin da ta riga ta yanke.

Kotun ta kuma bukaci lauyoyin jam'iyyar APC da kuma David Lyon da suka shigar da karar da su biya jami'iyyar PDP naira miliyan 60.

A ranar 14 ga watan Fabrairun 2020 ne Kotun Kolin ta soke nasarar Lyon da Eremionyo a zaben gwamnan Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.

Kotun ta soke zaben 'yan takarar na jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne a jajibirin ranar da su sha rantsuwar kama aiki.

A hukuncin kotun na baya, alkalan Kotun Kolin sun soke ce zaben Lyon ne saboda mataimakinsa ya mika wa hukumar zaben kasar takardun bogi domin ya samun tsayawa takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar 2019.