Almajirai sun bijire wa dokar Ganduje ta hana bara

Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara
Bayanan hoto,

Almajirai sun fito tituna suna bara bayan sanya dokar

Da alama mabarata sun bijire wa matakin da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta dauka na haramta bara a titunan jihar.

Ranar Talata ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga 'yan firamare da Sakandare a fadin jihar.

Sai dai kwana guda bayan gwamanti ta haramta bara, wakilin BBC ya zaga birnin na Kano inda ya ga mabarata na ci gaba da gudanar da barace-barace, kamar yadda za ku gani a wadannan hotuna da ya dauko daga sassa daban-daban na birnin Kano.

Bayanan hoto,

Almajirai sun fito tituna suna bara bayan sanya dokar

Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA ANWAR

Bayanan hoto,

Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai tallafa wa makarantun allo amma dole ne a fara koyar da turanci da lissafi

Matashiya

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta haramta bara a titunan jihar.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka yayin bikin mika takardun daukar aikin malanta ga mutane 7,500 a birnin Kano.

Ganduje ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga 'yan firamare da Sakandare a fadin jihar.

Ya ce daga yanzu dole ne makarantun allo su shigar da darussan turanci da lissafi cikin tsarin koyarwarsu.

Gwamnan ya ce "idan har kana zaton cewa ba za ka karbi tsarin nan na mu ba, to sai dai ka bar jihar."

A yayin jawabin, Ganduje ya bayyana cewa daga yanzu duk yaron da aka kama yana bara to za a kamo mahaifinsa ko mai kula da shi, kuma a gurfanar da shi gaban kotu saboda rashin mutunta dokokin

jihar.

Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA ANWAR

Bayanan hoto,

Wasu alkaluma na nuna cewa akwai fiye da yara Miliyan uku da ba sa zuwa makaranta kuma mafi yawansu a arewacin Najeriya suke

Ko a makon jiya ma sai da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatoci da su ringa kama duk wani mahaifi da aka samu dansa yana bara da sunan karatun Alkur'ani.

Matsalar bara musamman ga yara kanana na daga abinda ake dauka a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin dake addabar arewacin Najeriya.

Wasu alkaluma na nuna cewa akwai fiye da yara Miliyan uku da ba sa zuwa makaranta, kuma mafi yawansu suna yankin arewacin kasar ne.

A baya ma gwamnatoci a jihar ta Kano sun taba hana bara, sai dai matakin bai yi tasiri ba, saboda abinda wasu masana ke cewa rashin ingataccen tsari da tanadi.