Saudiyya za ta kaddamar da gasar kwallon kafa ta mata zalla

A watan Janairun 2018 ne aka fara barin mata domin shiga filin kwallo su yi kallo Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A watan Janairun 2018 ne aka fara barin mata domin shiga filin kwallo su yi kallo

Saudiyya za ta kaddamar da gasar kwallon kafa ta mata zalla, shekaru biyu bayan kasar ta fara barin matan su halarci filin kwallo domin kallo.

Za a fara buga gasar ne a Riyadh, babban birnin kasar da kuma wasu garuruwa biyu na kasar.

Kirkiro gasar na daga cikin sabbin tsare-tsare na da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya yi a kasar ta Saudiyya, kasar da ake ganin na daga cikin kasashen da ke da tsauraran dokoki.

Masu rajin kare hakkin dan adam dai na cewa har yanzu akwai sauran abubuwan da suka kamata a yi dangane da hakkokin mata.

Mahukunta a kasar sun bayyana cewa babban makasudin fitar da wannan sabon tsarin shi ne karfafa wa mata gwiwa domin shiga harkar wasanni.

A watan Janairun 2018 ne aka fara barin mata domin shiga filin kwallo su yi kallo - a kuma shekarar ce aka cire takunkumin da aka yi wa matar tun asali na hana su tukin mota.

A shekarar da ta gabata ne wata doka da ta fito da ga fadar Sarkin Saudiyya ta halarta wa matan kasar su yi tafiya ba tare da muharrami ba kuma an halarta musu zuwa gidan cin abinci ko babu muharrami.

Duk da haka, gwamnatin kasar ta kama masu kare hakkin mata da dama a kasar duk da wadannan tsare-tsaren da ta yi a kasar.

Labarai masu alaka