An yi wa Hosni Mubarak jana'izar girmamawa

Sojojin kasar Masar na mika gaisuwa a lokacinda ake wucewa da gawar Hosni Mubarak zuwa masallacin Tantawi da ke birnin Alkahira (26 Fabrairu, 2020) Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban kasar Masar na yanzu ya yi jinjinar ban girma ga Mubarak a lokacin faretin jana'izar sojin da aka yi wa marigayin

An yi wa tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak jana'izar soji, bayan ya rasu yana da shekara 91.

Shugaba Abdula Fattah al-Sisi tare da 'ya'yan marigayin sun yi wa gawar tsohon shugaban rakiya zuwa masallaci domin yi wa mamacin sallar jana'iza.

Gwamnatin Masar ta ayyana zaman makoki na kwana uku a fadin kasar.

A 2011 ne Hosni Mubarak ya sauka daga mulki bayan shekara 30, sakamakon zanga-zangar guguwar sauyin kasashen Larabawa.

Bayan nan tsohon shugaban ya yi shekara shida a tsakanin gidan kaso da asibitin sojin kasar, yayin da ake tuhumarsa da aikata wasu laifuka.

A 2012, an yanke wa Hosni Mubarak hukuncin daurin rai da rai saboda samun sa da hannu a kisan masu zanga-zanga.

Kotu ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekara uku saboda wawure kudaden gwamnati.

Kafafen yada labaran kasar sun ce tsohon shugaban ya rasu ne bayan an yi masa aikin fida a asibiti.

Ra'ayoyin 'yan Masar a kan Mubarak

Daga Sally Nabil, BBC News, Cairo

Wasu 'yan kasar sanye da bakaken kaya sun yi ta daga kwalaye masu dauke da rubutun yabon Mubarak a matsayin ''shugaba na gari'' sun yi dafifi a filin masallacin da aka yi masa sallah.

''Mutum ne mai basira da ya samar da daidaito na shekara 30 a kasar nan,'' in ji wani matashi.

Mubarak ya ba da muhimmaci ga samar da zaman lafiya. Yana kuma tinkaho da samar da kwanciyar hankali a tsawon shugabanci. Amma masu sukarsa na ganin hakan ya kuntata wa mutane da dama.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masoyan Hosni Mubarak sun yi cincirindo a Masallacin Tantawi

'Yan kasar Masar da suka yi wa Mubarak bore a 2011 na zargin gwamnatinsa da kama karya da kuma kawo matsalolin da suka dabaibaye kasar a lokacin.

''Duk daga cikin miyagun ayyukansa ne,'' in ji wani matashi.

Masu sharhi a shafukan zumunta na mamakin yadda aka yi wa Mubarak jana'izar ban girma bayan samunsa da laifin rashawa.

Sun yi mamakin hakan, ganin yadda aka binne magajin Mubarak, wato Mohammed Morsi, wanda ya rasu a shekarar 2019 a kotu, a cikin dare wanda danginsa kadai gwamnati ta bari suka halarta.

Morsi mai ra'ayin addinin Islama ne, shi kuma Mubarak jami'in sojin kasar ne - kuma sojoji ne suka mamaye fagen siyasar Masar a tsawon shekara 60.

Yayin da 'yan kasar ke daukar marigayi Mubarak a matsayin gwarzo, har yanzu 'yan kasar da dama na ganin gwamnatinsa ta fi ta yanzu bayar da 'yanci a kasar.

Shugaba Abdul Fattah ya mika ''sakon taziyya'' ga iyalan Hosni Mubarak.

A sakon ta'aziyyar da gwamnatin kasar ta fitar, ta yaba gudummuwar da Mubarak ya bayar a matsayin jami'in soji a lokacin yakin Isra'ila da kasashen Larabawa na 1973.

Sai dai sanarwar ba ta ambaci shugabancin da Mubarak ya yi a kasar ba.

''Yana daga cikin gwarazan yakin Oktoba da muka yi nasara, sadda ya jagoranci sojin sama a yakin da ya dawo da martabar kasashen Larabawa,'' a cewar sanarwar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Abdul Fattah al-Sisi (a tsakiya) tare da wasu manyan jami'an gwamnati

Shugaba Sisis shi ne tsohon shugaban hukumar tara bayanan sirri ta Masar kuma wanda ya jagoranci hambarar da zababbiyar gwamnatin magabacinsa, wato Mohammed Morsi a shekarar 2013.

Tun bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta jagoranci murkushe 'yan tawaye, tare da tsare dubban mutane, wasunsu a yanke musu hukuncin kisa, baya ga wasu da dama da suka yi batar dabo.