Da gaske an samu bullar coronavirus a Najeriya?

Cutar Corononavirus Hakkin mallakar hoto Getty Images

Asibitin Reddington a Lagos ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa akwai wani dan China da aka kwantar a asibitin mai dauke da cutar coronavirus.

A sanarwar da ya fitar, duk da babban daraktan asibitin Dr Olutunde Lalude, bai musanta zuwan dan China ba a asibitin domin diba lafiyarsa amma ya ce ba ya dauke da cutar mai yin kisa a China.

"Da safiyar Laraba ne dan Chinan ya kawo kansa asibitin Reddington a Ikeja inda ya ce yana fama da zazzabi, kuma bayan bincike an gano cewa ya shigo Najeriya daga China makwanni bakwai da suka gabata, kuma ba shi dauke da cutar," in ji shi.

Labarin bullar cutar Coronavirus a Najeriya ya mamaye shafukan intanet inda ake ta yada jita-jitar cewa cutar ta bulla a Lagos bayan kwantar da wani dan China a asibitin Reddington da ke Ikeja.

Babu dai wata sanarwa daga hukumomin Najeriya game da labarin, amma asibitin Reddington ya ce ya sanar da hukumomin lafiya na jihar Lagos.

Sanarwar da asibitin ta fitar ta jaddada cewa babu wani mai dauke da cutar coronavirus a dukkanin rassan asibitin.

Sanarwar ta kara da cewa lokacin da dan Chinan ya gabatar da kansa a asibitin, an yi kokarin killace shi kamar yadda asibitin ya yi tanadi kan duk wani marar lafiya da ake tunanin barazanar coronavirus tare da shi.

"An sanar da hukumomin lafiya, sannan an dauki jininsa zuwa wurin babban gwaji na gwamnatin Lagos," in ji sanarwar.

Sai dai kuma sai zuwa gobe ne sanarwar ta ce ake sa ran samun sakamakon gwajin da aka yi masa.

Zuwa yanzu an kwantar da dan Chinan a asibitin da ake kula da cututtuka masu yaduwa a Lagos yayin da ake jiran sakamakon gwajin.

Asibitin dai na nufin zuwa yanzu ba a tabbatar da ko dan Chinan yana dauke da cutar coronavirus ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tuni Gwamnatin Najeriya ta dauki matakai na gwajin bakin da suka shigo Najeriya a filayen jiragen sama

Cutar ta kashe mutum 2771 a duniya, kuma ta fi yin kisa ne a China inda cutar ta bulla yayin da kuma take ci gaba da bazuwa zuwa wasu kasashe.

Aljeriya ta shiga jerin kasashen duniya da aka samu bullar cutar ta da ake kira COVID-19, kasa ta biyu da aka samu bullarta a Afirka bayan Masar.

Labarai masu alaka