Coronavirus: Kakakin Buhari ya soki jaridun Najeriya

.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya soki jaridun Najeriya saboda mayar da hankali da suka yi na bayar da labarai kan coronavirus maimakon cutar zazzabin cizon sauro.

Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi inda ya ke jan hankalin 'yan jaridu kan sai yaushe za su mayar da hankali kan 'yan Najeriya 822 da ke mutuwa sakamakon cutar zazzabin cizon sauro a kullum.

BBC ta tuntubi Malam Garba Shehu domin jin karin bayani dangane da wannan batu, sai dai ya bayyana cewa wannan ra'ayinsa ne ya bayyana ba wai ra'ayin fadar shugaban kasa ba.

Kalaman na Garba Shehu na zuwa ne a daidai lokacin da wasu manyan kasashen duniya ke kokarin yaki da wannan cuta wadda ta zama alakakai a kasashen.

A ranar Juma'a ne aka tabbatar da bullar cutar a Najeriya, sai dai hukumomi a kasar sun shaida cewa suna iya bakin kokarinsu wajen dakile yaduwar cutar.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.