Cikin Hotuna: Kannywood a makon jiya

Ga hotunan wasu abubuwan da suka faru a masana'antar Kannywwood da muka zabo muku daga makon da ya gabata:

Hakkin mallakar hoto @officialkannywoood
Image caption Taron shugabanni da Kwamitin Amintattun kungiyar masu shirya fina-finai a Arewacin Najeriya ya amince da a hada kai, a yi magana da murya daya domin kawo gyara da ci gaban Kannywood da kuma cimma manufofin masana'antar fim da masu sana'a ar a yankin.
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption A nan wasu jarumai ne da suka fito a matsayin sojoji dauke da manyan bindigogi bayan sun diro daga jirgin yaki a wani sabon fim da ake kan dauka, wanda Yakubu Mohammed, Usman Uzee da Funky Mallam da sauransu suka fito a ciki.
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption Sabon fim din barkwanci mai suna 'Ajebon Ghetto', na Adam A. Zagno
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption Ana ci gaba da daukar shirin 'Kwana Casa'in' Zango na uku wanda ake sa ran fara nunawa a cikin watan Afrilu mai kamawa.
Hakkin mallakar hoto @officialkannywood
Image caption Ana ci gaba da daukar shirin 'Kwana Casa'in' Zango na uku wanda sa ran fara nuna shirin a cikin watan Afrilu mai kamawa.
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption Kamfanin FKD mallakin Ali Nuhu ya cika shekara 20 da kafawa. An yi ta taya FKD murnar daga ciki da wajen Kannywood, yayin da kamfanin ya ce nan gaba zai sanar da ranar shagalin bikin cikarsa shekara 20.
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption Abba El-Mustapha a lokacin daukar sabon fim da zai fito nan gaba, mai suna "Ba amo", wanda Naziru Danhajiya ya shirya, da kuma Ali Gumzak a matsayin Darekta.
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption Shin Daushe ya koma sana'ar tukin babbar mota ne, ko kuma dai fasinja ne shi a wannan rokar? Me ya sami madubin motar?
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption Ali Nuhu ya yi maraba tare da godiya ga manyan baki kuma abokan sana'arsa wato Umar M. Shareef da Classiq a sadda suka je yin siyayya a shagonsa.
Hakkin mallakar hoto @instagram
Image caption Wurin daukar wani sabon fim mai suna "Hikima", wanda Alhaji Shehe ya shirya, Hafizu Bello kuma ke a matsayin darekta.
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption A makon da ya gabata ne aka yi bikin zagayowar ranar auren tauraron Kannywood Ishaq Sidi Ishaq da mai dakinsa.
Hakkin mallakar hoto @kannywoodcelebrities
Image caption Wa ya gane mai wainar nan? Ko za ku tuna a fim din da ta yi tuyar waina?