Najeriya: An gano wadanda suka yi hulda da mai coronavirus

@

Asalin hoton, Getty Images

An gano sama da mutum 100 a Najeriya da suka samu kusanci da dan kasar Italiyan da ke dauke da cutar coronavirus a kasar.

Kwamishinan lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya ce hukumomin kasar sun tuntubi mutanen da ake kyaututa zaton sun yi hulda da mara lafiyan.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ta ambato kwamishinan na cewa adadin mutanen da ake tantancewa saboda sun yi mu'amala da mutumin na iya karuwa.

Yanzu mara lafiyan wanda dillali ne na kamafin siminti na Lafarge da ke Ogun, na killace a cibiyar kula da masu coronavirus da ke Yaba a jihar Legas.

Mutumin ya isa Najeriya ne a ranar 24 ga watan Fabrairu ta filin jirgin sama da ke Legas kafin washegari ya wuce jihar Ogun mai makwabtaka.

Kwanansa biyu a Najeriya kafin a gano alamun coronavirus a tare da shi, sannan aka killace shi.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.