Abin da Buhari ya ce a kan cutar coronavirus

@

Asalin hoton, @NGRPresident

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi magana a kan cutar coronavirus da aka samu bullar ta a kasar.

Buhari ya yaba wa Ma'aikatar Lafiyar kasar da Hukumar Hana Yaduwar Cututtka, NCDC da gwamnatocin jihohin Legas da Ogun bisa matakan da suka yi gaggawar dauka a kan cutar.

Ya kuma shawarci 'ya kasar da su bi matakan kariya da Ma'aikatun Lafiya da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO da NCDC suka bayar domin kare kawunansu daga kamuwa da coronavirus.

A sakon da fadar shugaban kasar ta fitar, Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su daina nuna karaya ko tayar da hankalin game da cutar domin yin hakan na da illa sosai.

Sakon shugaban na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan wasu 'yan kasar sun yi ca a kan mai magana da yawunsa kan wani sako da ya wallafa a Twitter, inda ya zargi jaridun kasar da rashin mayar da hankali kan mace-macen da ke samu a kasar ta dalilin zazzabin cizon sauro.

Mutumin da aka fara samu yana dauke da coronavirus a Najeriya ya bar jihar Legas zuwa jihar Ogun ne bayan shigowarsa kasar daga Italiya.

A jihar Ogun din ne alamomin cutar suka fara bayyana kafin daga bisani a killace shi a Legas.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.