Shugaban Argentina na so a halasta zubar da ciki

Argentine women at a rally to demand legalisation of abortion in Argentina, 19 February 2020

Asalin hoton, EPA

Shugaban Argentina Alberto Fernández ya ce zai aike da wani kudurin doka da zai nemi halasta zubar da ciki ga majalisar dokokin kasar nan da kwana goma masu zuwa.

Mr Fernández, wanda ya sha rantsuwar kama aiki a watan Disamba, ya taba bayyana zubar da ciki a matsayin "al'amarin da ya shafi lafiyar mutane."

A Argentina, an halasta zubar da ciki ne kawai ga matan da aka yi wa fyade, ko kuma idan lafiyar mai cikin na fuskantar barazana.

An haramta zubar da ciki a akasarin yankin Latin Amurka, idan ban da 'yan wurare kadan.

Idan aka amince da kudurin dokar, Argentina za ta kasance kasa mafi girma a yankin da ta halasta zubar da ciki.

"Ana zubar da ciki, ba wani abu ba ne," a cewar shugaban kasar a jawabinsa na farko ga zauren majalisar.

"Ya kamata kasa ta kare 'ya'yanta gaba ki daya da kuma mata musamman. A wannan karni na 21, ya kamata kowacce al'umma ta girmama zabin da 'ya'yanta suka yi wa kansu kan yadda za su yi amfani da jikinsu."

Mr Fernández ya kuma yi alkawarin bullo da wani shiri da zai rika ilimantar da 'yan kasar game da mu'amalar aure.

Yunkurin da aka yi a baya na sauya dokar zubar da cikin bai yi nasara ba a kasar, wacce galibin mazauna cikin ta mabiya darikar Roman Katolika ne.

Asalin hoton, EPA