Yadda rikicin Addini ya shafi mata Musulmi a India

Mata da yara sun nemi mafaka a Indira Vihar

Asalin hoton, Bushra Sheikh

Mummunan rikicin addinin da ke faruwa a wasu sassan babban birnin Indiya Delhi ya sanya rayuwar mata da kananan yara a cikin tsaka mai wuya.

Rikicin wanda ke faruwa a arewacin Delhi ya janyo mutuwar mutum 40 da suka hadar da 'yan bangaren Hindu da Musulman kasar.

Dubban musulmai mata da yara sun bar gidajensu.

A wani katafaren dakin taro, akwai cuncurundon mutane da suka hada da mata da yara a Indira Vihar wadanda suka bar gidajensu saboda rikicin.

Wadannan mutane na zaune a kan darduma da tabarmai.

Dakin taron na wani dan kasuwa ne Musulmi abin da yanzu ya zama mafaka ga wadanda suka rasa muhallansu.

Matan sun bar gidajensu ne saboda hare-haren da 'yan addinin Hindu ke kai wa gidajensu a Shiv Vihar, daya daga cikin wuraren da rikicin yafi kamari.

Wata unguwar kananan ma'aikata wacce mabiya addinin Hindu suka fi rinjaye amma mai musulmai da dan dama Shiv Vihar, cike take da matsattsun lunguna kusa da wata katuwar lamba 2.

Mita 200 daga waccan unguwa ta Shiv Vihar a gefen lamba 2, unguwannin Chaman Park da Indira Vihar ne inda Musulmai ke da rinjaye, hanya ce kawai ta raba yankin da ke da mabiya addinin Hindu masu rinjaye da kuma inda Musulmai masu rinjaye suke.

Sun shafe gomman shekaru suna zaman lafiya a tsakaninsu, amma a yanzu abin ya sauya.

Asalin hoton, Bushra Sheikh

Bayanan hoto,

Nasreen Ansari a hagu tare da mahaifiyarta Noor Jehan Ansari

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Nasreen Ansari, na daga cikin wadanda suka tsere suka bar gidajensu da ke Shiv Vihar, ta ce rikicin ya fara ne tun daga ranar Talata da rana a lokacin mata ne kawai a gida.

Ta ce a lokacin mazan yankin sun tafi wani wajen taron addini da ake cewa Ijtema.

Nasreen Ansari, ta ce " Mun hango maza 50 zuwa 60, ko da na hango su ban san ko su waye ba, don ban taba ganinsu ba, sun shaida mana cewa sun zo ne domin su taimake mu don haka mu zauna a cikin gida".

Ta ce ita da sauran matan da suke zaune a gida sai suka hange ta taga da baranda daga nan ne suka gane cewa wadannan mazan ba taimakon su suka zo yi ba.

Mazan sun sanya hular kwano sannan kuma sun rike sanduna.

Nasreen ta ce, mazan na yin take irin na 'yan Hindu kamar Jai Shri Ram.

Can suna zaune sai wata makociyarsu ta kira mamanta a waya ta ce mata ai an cinna wa gidansu wuta.

Nasreen ta ce, "Ta tagar gidanmu muna hango yadda aka kona gida da shagon wani makocinmu".

Ta ce maharan wadanda 'yan bangaren addinin Hindu ne, sun lalata taransifomar da ke bamu hasken lantarki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dubban mutane sun tsere daga Shiv Vihar

Ta ce ba mu yi aune ba sai kawai muka ga mutanen suna ta cilli da tukunyar gas suna kona shaguna wadanda mallakin Musulmai ne, amma ba sa taba gidajen 'yan Hindu.

Nasreen ta ce "Ban taba tunanin wani abu kamar haka zai faru ba a yankinmu".

Ta ce mata Musulmai na yankin suka rinka kiran 'yan sanda, amma sai su rinka ce musu suna nan zuwa nan da 'yan mintuna kadan, amma kuma shiru kake ji.

Nasreen ta ce da farko sai da ta kira wasu 'yan uwansu ta shaida musu cewa yau fa sai yadda hali ya yi.

To amma daga bisani an kubutar da su bayan da 'yan sanda suka rako Musulman mazan yankin da suka dawo daga taron da suke je.

Nasreen ta ce "Mun bar gidajenmu ba tare da daukar komai ba".

Shira Malik 'yar shekara 19, sun samu mafaka ita da 'yan gidansu a makotansu, ta ce sun makale a can an jefe su da duwatsu.

Bayanan hoto,

Shira Malik a hagu, sun samu mafaka a makota

Yawancin mata Musulman da suka nemi mafaka sun shaida wa BBC cewa, 'yan Hindun da suka kai hari yankinsu sun ci zarafinsu ta hanyar cire musu mayafai da yaga musu kayan jikinsu.

Wata mata ta ce wata makociyarta 'yar addinin Hindu ce ta cece ta bayan da shaida wa maharan cewa ita ba Musulma ba ce.

An dai fara rikicin ne a yammacin ranar Lahadi a wani waje da ba shi da nisa da Shiv Vihar bayan musu ya kaure tsakanin magoya bayan dokar 'yancin zama dan kasa a Indiya da kuma wadanda ke adawa da dokar.

Kafin ka ce kwabo rikicin ya fadada zuwa unguwannin da ke makwabtaka da wajen ciki har da Shiv Vihar da Chaman Park.

Asalin hoton, Bushra Sheikh

Bayanan hoto,

Many of the women said how close they came that night to being sexually assaulted

An dai girke jami'an tsaro a wuraren da rikicin ya fi kamari domin tabbatar da cewa babu wani rikici da ya kara barkewa.

Ga matan da ke zaune yanzu haka a Indira Vihar domin neman mafaka, sun ce ba su san ranar da za su gidajensu ba.

Shabana Rehman, ta ce 'ya'yanta suna yawan tambayarta cewa yaushe za su koma gida.

Ta ce " An kona mana gida ina za mu je? Mece ce makomar 'ya'yana? Wa zai duba mu?Mmun rasa komai namu hatta takardunmu".