'Yan bindiga sun kashe Hakimi a Zamfara

Babban Sufeton 'yan sanda

Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE

Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun kashe Hakimin wani kauye a karamar hukumar Maru.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya tabbatar wa BBC cewa 'yan bindiga sun kashe hakimin kauyen Kujemi da ke yankin Dansadau ne ranar Lahadi.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Mohammed Shehu, ya ce an kashe Malam Gambo Kujemi da wani mutum daya.

SP Shehu ya kara da cewa an kashe hakimin, wanda yake ziyara a Karauchi a yankin na Dansadau, lokacin da 'yan bindigar suka kai hari a kauyen da almurun ranar Lahadi.

Kakakin 'yan sandan ya ce ana kan bincike kan lamarin.

Jihar ta Zamfara na cikin jihohin da aka fi fuskantar matsalar 'yan bindiga da masu satar mutane domin kudin fansa.