‘Na taba yin gadi amma yanzu na zama minista’

Suleiman Yusuf Koore

Asalin hoton, Suleiman Yusuf Koore/Facebook

Ba kasafai ake samun labarin cewa mai gadi ya rike mukamin minista a gwamnati ba.

Amma a yankin Somaliya, Suleiman Yusuf Koore mai gadi ne a da, sai dai a yanzu ya zama minista.

Ya fara gadi ne a shekarar 1984 a matsayin mai gadin gidan rediyon gwamnatin Hargeisa, kuma ginin gidan rediyon yana cikin ma'aikatar yada labaran kasar.

A yanzu Suleiman shi ne ministan yada labaran Somaliya, ma'ana shi ne ya fi kowa matsayi a ma'aikatar yada labaran kasar.

Mr Koore ya ce "A lokacin da nake gadi ba a bari na shiga ofishin da nake zama a yanzu a matsayin minista saboda ni mai gadi ne a wancan lokacin".

A lokacin da yake gadi albashinsa bai wuce dala 12 ba, amma a yanzu a matsayin minista, albashinsa a wata ya kai dala dubu biyu ban da alawus din dala 750 duk wata.

Mr Koore dai ya jima ana damawa da shi a siyasar kasar domin ya shafe shekara 25 yana harkokin siyasa; haka kuma ya rike mukamai da dama, kafin a ba shi minista yanzu.

Ministan ya ce "Abin alfahari ne a gare ni na zamo ministan ma'aikatar da na yi wa aiki a lokacin da nake matashi."