Da gaske muke son magance bazuwar makamai - Gwamnatin Najeriya

Osinbajo

Asalin hoton, Osinbajo Twitter

Bayanan hoto,

A ranar Litinin ne mataimakin shugaban kasar ya jagoranci taron

Gwamnatin Najeriya ta ce da gaske take kan batun magance bazuwar haramtattun makamai a kasar.

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin bitar rahoton kwamitin shugaban kasa kan bazuwar makamai.

Najeriya dai na fama da matsalar tabarbarewar tsaro, inda ko a ranar Lahadi sai da wasu da ake zargin 'yan fashin daji ne suka aukawar garin Kerawa a cikin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna tare da hallaka kimanin mutum 50.

Abdurrahman Baffa Yola, mataimaki na musamman ne a fadar shugaban Nijeriya, ga kuma karin bayanin da ya yi wa Mukhtari Adamu Bawa:

Bayanan sauti

Hira da Abdurrahman Baffa Yola

Asalin hoton, Osinbajo Twitter

Asalin hoton, Osinbajo

Asalin hoton, Osinbajo