Corona: Farashin man goge hannu da takunkumin rufe fuska sun tashi a Lagos

face mask

Asalin hoton, Getty Images

Al'ummar jihohin Lagos da Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya sun fara kokawa kan tashin farashin man goge hannu don hana kamuwa da cututtuka da kuma takunkumin rufe baki da hanci, wadanda ake rububin amfani da su saboda yaduwar coronavirus.

Mutane na ta korafi cewa masu shagunan magunguna wato kemis, sun tsauwala farashin man goge hannun wanda ya tashi daga naira dubu 2,500 zuwa dubu 19,000.

Wani abin da shi ma ya kara farashi shi ne na takunkumin rufe baki da hanci domin samun kariya daga harbuwa daga cutar.

Wakilin BBC a Legas Umar Shehu Elleman ya jiyo ra'ayoyin mutane a game da matakan da suke dauka kan hauhawar farashin.

Wani mutum ya ce: "Kalubalen da muke fuskanta a yanzu shi ne farashin man shafawa a hannu domin samun kariya daga harbuwa da cuta ya yi sama.

"A jiya, wani ya so ya sayi man wanda a baya farashinsa bai kai naira dari biyar ba, to amma sai aka ce masa naira dubu N 19,000. Kuma a lokacin da ya je manyan shaguna kamar Shoprite ya samu man ya kare.

"To amma mun sami bayani daga jami'an lafiya cewa ba dole ba ne sai mun yi anfani da wannan man ba, in har za mu ke wanke hannuwanmu sau shida zuwa sau bakwai da ruwa mai kyau a kowace rana to babu matsala.

"Ina gani ya kamata mu watsa wannan bayani ga jama'a domin dai kar hankalin mutane ya tashi."

Shi kuwa dayan cewa ya yi: "Ba na anfani da wani abu domin samun kariya daga wannan cuta don kuwa babu kudi da zan sayi maganin.

"Matsalar ita ce mutane da yawa ba su da kudin da za su saya domin kare kansu daga cutar, dubu 19 ba kananan kudade ba ne.

Wata matar kuma cewa ta yi: "Ni dai ina iya kokarina domin tabbatar da cewa ban sha hannu da mutane ba, sa'annan na kan wanke hannuna akan kari.

"Na ji labari cewa farashin man shafawa a hannu domin samun kariya daga harbuwa da cututtuka ya kai naira dubu 19,000."

Amma da wakilin namu ya je wani shago ya ce ana samun dan karami a kan dubu daya yayin da matsakaici kan kai dubu 4,500.

Mutane na amfani da wannan man domin kaucewa kwasar kwayoyin cuta yayin musabaha da wani mutum da ke dauke da cutar ko kuma ya yi mu'amala da wani da ke dauke da cutar.

A hannu guda kuma hukumomin lafiya a jihohin Legas da Ogun inda mutumin dan kasar Italiya da ke dauke da cutar coronavirus ya yi cudanya da su, sun kara tsananta matakan inganta harkokin lafiya a wasu cibiyoyi na musanman da su ka kebe.

Wannan kuwa har da kamfanin buga siminti na Lafarge da ya je yi wa aiki a jihar Ogun.

Wasu dai na da ra'ayi cewa baya ga yunkuri daga gwamnatin tarayya akwai bukatar jihohin Naijeriya da su hada kai domin tunkarar wannan cuta da zuciya daya domin dai a gudu tare a tsira tare.

Kawo wannan lokaci hukumomin lafiya a jihohin Legas da Ogun ba su nuna an samu karin wani ko wata da suka kamu da cutar ta coronavirus ba, face mutumin na farko dan kasar Italiya da ya zo yi wa kamfanin buga siminti na Lafarge aiki a jihar Ogun.

To sai dai akwai daruruwan mutane da ake bibiyar al'amuransu bayan an gano sun yi mu'amala da mutumin walau a cikin jirgi ko a otel ko a cikin mota ko kuma wuraren cin abinci.

Sai dai hukumar lafiya a jihar Legas tun a karshen mako ta karyata rahotannin da ke ta watsuwa cewa mutumin mai dauke da cutar ya yi yunkurin tserewa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Takunkumin rufe fuska na daga cikin abin da ake rububi