Muhimmancin 'Super Tuesday' a zaben Amurka

 • Daga Roland Hughes & Holly Honderich
 • BBC News
Joe Biden campaigning in Virginia

Asalin hoton, EPA

Masu zabe a fadin Amurka na shirin zaben fitar da gwani na karshe a jam'iyyar Democrat a Babbar ranar Talata mafi muhimmanci ta zaben 2020.

Sama da shekara daya bayan dan takara na farko a jam'iyyar Democrats ya shiga takara domin karawa da Donald Trump, yanzu an zo ranar Talata mai muhimmanci wadda a ranar ne za a fitar da zakara.

Jihohi 14 ne dai za su jefa kuri'a domin fitar da wanda zai yi musu takara daga jam'iyyar Democrats. Bernie Sanders shi ne kan gaba a zaben fitar da gwani da aka fara a farko.

A ranar Laraba, za a san wanda zai tsaya wa jam'iyyar takara.

Abin da ke faruwa zuwa yanzu

'Yan jam'iyyar Democrats a fadin kasar na yin tarurruka na masu ruwa da tsaki domin fitar da wadanda suke gani za su kai su ga nasara.

Nasarar da Bernie Sanders ya samu ba ta zo da mamaki ba.

Hillary Clinton ta kayar da shi a shekarar 2016, sai dai shi ba mai ra'ayin rikau ba ne a jam'iyyar Democrats, sakamakon ko a majalisar dattawan kasar bai cika daukar bangare ba.

Yana daga cikin masu akidar kawo sauyi. Shekarunsa 78 kuma ya taba samun bugun zuciya, amma duk da haka ya yi fice a zaben fitar da gwani kuma da alama mutane da dama na goyon bayansa.

Wasu daga cikin masu takarar 'yan Democrats sun raba kuri'un a tsakaninsu, wanda hakan ya sa Mista Sanders ke kan gaba.

Daya daga cikinsu shi ne tsohon mataimakin shugaban kasa wato Joe Biden.

Me ya sa Babbar ranar Talata ke da muhimmanci?

Wakilan jam'iyya ko Delegates, su ne ke da muhimmanci a wannan rana.

Misali idan aka ce dan takara na farko na da cikakken goyon baya a wata jiha, dan takara na biyu kuma yana da goyon baya amma ba sosai ba, wannan zai sa dan takara na farko ya zamo yana da wakilai mafi yawa.

Sai dai yawan delegate ko wakilan jam'iyya a kowace jiha ya bambanta.

Wannan ne dalilin da ya sa Babbar ranar Talata ke da amfani a zaben 2020.

Har yanzu, masu zaben fitar da gwani ko kuma wakilai 155 ne kawai aka fitar a jihohi hudu.

A Babbar ranar Talata, wakilai masu dimbin yawa da suka kai 1,357 za a fitar kuma jihohi 14 ne za su yi zaben.

Jihohi biyun nan da suka fi yin suna wato Texas da California za su shiga cikin zaben.

Yawan Wakilan jam'iyya daga jihohi 14

 • VERMONT - 16
 • MAINE - 24
 • UTAH - 29
 • ARKANSAS - 31
 • OKLAHOMA - 37
 • ALABAMA - 52
 • TENNESSEE- 64
 • COLORADO - 67
 • MINNESOTA - 75
 • MASSACHUSETTS - 91
 • VIRGINIA - 99
 • NORTH CAROLINA - 110
 • TEXAS - 228
 • CALIFORNIA - 415

Wasu wakilai shida daga daga American Samoa da wasu 'yan Democrats 13 daga ketare da su yi zabe a Babbar ranar Talata.