Hotunan zanga-zangar nakasassu a Abuja

Nakasassu

Mambobin kungiyar nakasassu sun gudanar da wata zanga-zanga a Abuja, babban birnin Najeriya.

Mambobin kungiyar daga jihohi 36 a kasar ne suka halarci zanga-zangar da aka gudanar ranar Talata.

Masu zanga-zangar sun taru ne a gaban ofishin hukumar NDLEA da ke babban birnin, inda suka bukaci a dauke su aiki.

Sun ce sun yi haka ne saboda sabuwar dokar masu bukata ta musamman da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a baya-bayan nan, wadda ta bukaci a rika kebe musu kaso biyar cikin 100 na guraben aiki a kasar kuma a daina nuna masu wariya da dai sauran tanade-tanade.