Amurka za ta ba da tukwicin ₦2.5b kan Shekau

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi tayin cewa za ta ba da tukuicin dala miliyon bakwai kwatankwacin sama da naira biliyan biyu da rabi ga wanda ya ba da bayanin da zai taimaka wajen kama shugaban kungiyar Boko Haram Abubukar Shekau.

Amurka da mahukunta a Najeriya sun dade suna neman Shekau ruwa a jallo.

Ba wannan ne karon farko da Amurka da mahukunta a Najeriya suke irin wannan tayin ba.

Kazalika sojojin Najeriyar sun sha ikirarin kashe Shekau, amma daga bisani sai ya bulla a wasu hotunan bidiyo yana karyata su.

Mallam Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro a Najeriya da yankin Sahel, kuma ya bayyana wa BBC cewa babu wata shaida da za ta nuna cewa a wannan karon tayin da Amurka ta yi zai yi tasiri.

A cewarsa "kusan shekara shida kenan Amurka ta fara fitar da irin wannan sanarwar tayi" ga wanda ya gabatar mata da bayanai game da Shekau.

Ya ce "lallai babu shaidar cewa a cikin shekara shida Amurka ta samu wasu bayanai da za su taimaka mata."

Ya bayyana cewa akwai hanyoyin da ake bi wajen tattara bayanai da sarrafa su, "dole sai ka yi hakuri, a dauki lokaci mai yawa kafin ka cimma burin nasarar da kake son cimma."

"Idan ka duba yadda har suka gano Shugaban kungiyar Al Qaeda Usama Bin Laden sai da suka yi amfani da hanyoyi da yawa kafin daga baya suka cimma nasara." a cewarsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyar Boko haram ta fi shekara goma tana ayyukanta a Najeriya musamman ma a yankin arewa maso gabashin kasar

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mallam Adamu ya bayyana cewa yawancin masu shiga kungiyar ko wadanda suke kusa da shugabannin kungiyar, kudi bai cika yin tasiri a kansu ba, saboda akwai akidar da suke rike da ita.

"Idan akwai wadanda ke kewaye da shi wadanda kila ba su rungumi akidar ba, kudi zai iya tasiri a kansu,"

"Wadanda suke da masaniya kan inda Shekau yake, akidunsu da kuma inda suka sa alkibla bai zamo daya da gwamnatin Najeriya da Amurka ba,"

"Saboda yadda ita kanta gwamnatin Najeriyar ta fuskanci yakin wadanda suke da irin wannan masaniya basu yarda da tafiyar da ita kasar Amurka ta ke ba da gwamnatin Najeriya," kamar yadda masanin ya fada.

"Wurare uku ne ake hasashen cewa shugabannin wadannan kungiyoyi da sansanonin suke, tsakanin tafkin Chadi da iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru sai kuma cikin dajin Sambisa." in ji sa.

Da yake magana kan ja da bayan da wasu suke wajen ba da bayanan sirri, Malam Adam ya ce "rashin yarda da ke tsakanin jama'a da jami'an tsaro dalili ne wanda kusan binciken da aka yi ya zo daya, kuma har yau wannan matsala na nan."

Ya ce akwai bukatar a inganta yarda tsakanin jami'an tsaro da jama'a idan har ana so a cimma burin kama shugaban na Boko Haram.