Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekara 83

Shugaba Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo

Asalin hoton, Buhari da Obasanjo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo murnar cika shekara 83 a duniya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya aike wa manema labarai ta bayyana cif Obasanjo a matsayin mutumin da ya "sadaukar da rayuwarsa wurin yin hidima ga Najeriya, Afirka da kuma duniya baki daya."

"Shugaba Buhari ya bi sahun iyalai da abokai da makusantan tsohon shugaban kasa domin taya shi murna kan wannan tsawon rayuwa, inda ya kara da cewa fafutukar Cif Obasanjo wurin ganin Najeriya ta kasance dunkulalliyar kasa a bayyane yake kuma abin yabo ne," a cewar Shugaba Buhari.

Ya kara da cewa tsohon shugaban kasar ya tsaya tsayin daka wurin ganin wanzuwar mulkin dimokradiyya a Afirka da ma wasu kasashen duniya.

Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya ci gaba da bai wa Cif Obasanjo tsawon rayuwa da lafiya da kuma karfin bauta wa Najeriya da kuma kasashen Afirka.

A baya dai, tsohon shugaban kasar ya caccaki salon mulkin Shugaba Buhari, wanda ya bayyana a matsayin mutumin da ya kasa tafiyar da harkokin kasar.

Sai dai Shugaba Buhari ya sha yi masa raddin cewa yana bakin kokarinsa wajen magance matsalolin da ya ce tsoffin shugabanni irin su Cif Obasanjosuka jefa ta a ciki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Obasanjo ya taba cewa Shugaba Buhari bai iya tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar ba