Hotunan mummunar zaftarewar kasa sakamakon mamakon ruwan sama a Brazil

Firefighters dig for victims of a mudslide in Guarujá, São Paulo state, Brazil. Photo: 3 March 2020

Asalin hoton, Reuters

Presentational white space

Kimanin mutum 23 ne suka mutu a Brazil sannan fiye da wasu 30 suka yi batan dabo bayan mamakon ruwan sama da zaftarewar kasa a jihohin São Paulo da Rio de Janeiro.

Ana tunanin adadin mutanen da suka mutu zai karu yayin da masu agaji ke ci gaba da kokarin nemo mutanen da suka bata.

Asalin hoton, Reuters

Lamarin ya fi shafar São Paulo, inda kimanin mutum 18 aka ruwaito sun mutu.

Daga cikin mutanen har da wata mata da danta da kuma masu kashe gobara biyu.

Sun yi kokarin ceto wani yaro da baraguzai suka rufe shi sakamakon zaftarewar kasar a karo na biyu.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

A yankin Guarujá, gidaje da dama sun rushe sakamakon zaftarewar kasar.

Asalin hoton, Reuters

Mazauna yankin na taimaka wa masu aikin agaji wajen gano wadanda suka bata da kuma gyara wajen.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Zaftarewar kasar ta rufe tituna da yawa sannan bishiyoyi sun fadi kasa.

Asalin hoton, Reuters

Mazauna wajen na kokarin kwashe kayayyakin da suka mallaka.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

A makwabciyar jihar Rio de Janeiro, kimanin mutum biyar ne suka mutu.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Yankin kudu maso gabashin Brazil ya fuskanci matsalar ruwan sama mai karfi a lokacin zafi.

A watan Janairu, kimanin mutum 30 ne suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama a jihar Minas Gerais wadda ke makwabtaka da São Paulo.

Duk hotuna na da hakkin mallaka