Coronavirus ta sauya yadda jama'a ke gaisawa

  • Daga Fauziyya Kabir Tukur
  • BBC Hausa, Abuja
A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba John Magafuli da wani jagoran adawa a Tanzani suna sabuwar gaisuwa saboda Coronavirus

Cutar Coronavirus (Covid-19) ta bulla a sassa daban-daban na duniya tun daga watan Disambar 2019 da ta fara bayyana a birnin Wuhan da ke yankin Hubei na kasar China.

Masana sun gano cewa cutar wadda take shafar numfashi ana saurin daukar ta musamman idan mai dauke da ita ya yi tari ko atishawa a cikin mutane.

Kwayoyin cutar kan bi iska su shiga jikin wanda ke kusa da mai dauke da ita, ta ido ko ta hanci ko kuma ta baki.

Haka kuma, idan mai dauke da cutar ya taba fuskarsa, kwayoyin cutar na iya bazuwa zuwa tafin hannunsa daga nan kuma idan ya taba wani da hannun don gaisawa ko runguma zai iya ba shi cutar.

Idan aka kamu da cutar, a kan yi zazzabi mai zafi da tari da numfashi sama-sama.

Bayanan bidiyo,

An koma gaisawa ta hanyar hada kafa da kuma sauran sassan jiki

Ma'aikatan lafiya da hukumomin lafiya a fadin duniya sun yi gargadi kan yadda za a kare kai daga kamuwa da cutar ciki har da: rage taruwa a wuri guda, rage taba fuska, yin musabaha ko rungumar juna.

Wannan ya sa mutane a fadin duniya, musamman inda cutar ta bulla suka dauki wasu matakan kare kansu daga kamuwa da cutar.

Har kasashen da cutar Coronavirus ba ta bulla ba ma sun dauki matakan kariya.

Misali a Saudiya, kafin cutar ta bulla, gwamnatin kasar ta fitar da sanarwar hana baki shiga don yin aikin Umara duk don kada a samu bullarta a ciki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A kasashe da dama, mutane na sa irin wannan abin don rufe hancinsu da bakinsu

A kasashen da cutar ta bulla, mutane na sa abin rufe fuska don kare hancinsu da bakinsu, sannan wasu na sa safar hannu.

A wasu wuraren kuwa, dokar hana fita aka sa, misali a wasu sassan Italiya da aka samu yaduwar cutar.

Yin musabaha da rungumar juna na cikin manyan hanyoyin gaisawa a tsakanin al'umma.

Amma bullar cutar voronavirus ta sauya hakan, kuma ta ba da damar kirkiro sabbin hanyoyin gaisuwa da ba sai an hada jiki ba.

Musabaha da kafa

A shafukan sada zumunta, an yi ta yada hotunan bidiyo da ke nuna mutane suna gaisawa ta hanyar hada kafa a madadin hada hannuwa kamar yadda aka saba.

An yi wa wannan salon gaisuwar lakabi da 'Wuhan Handshake' wato musabahar Wuhan, wato garin da cutar ta samo asali.

Asalin hoton, Getty Images

Daga baya, shugabannin duniya kamar John Magafuli na Tanzania sun dauki wannan salon gaisawar duk da cutar ba ta bulla a kasar ba.

A wani hoton bidiyo ministan harkokin cikin gidan Jamus ya ki yin musabaha da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a lokacin wani taro bayan ta mika masa hannu.

Gaisuwa da gwiwar hannu

Wani sabon salon gaisuwar da ya fito shi ne gaisuwa da gwiwar hannu wanda aka yi wa lakabi da 'Elbow bump'.

Ma'abota shafukan sada zumunta da dama musamman a shafin Twitter sun wallafa sakonni da maudu'in #elbowbump.

Wannan salon gaisuwar dai ya fi yawa a Amurka.

Wasu na ganin wannan ita ce hanya mafi a'ala da za a gaisa salin-alin ba tare da an yada cutar Coronavirus ba.

Gaisuwar 'Namaste'

Hada tafukan hannuwa wuri daya sannan a sa su a gaban kirji, kamar yadda 'yan kasar Indiya ke yi, wata hanya ce da mutane ke ta amfani da ita wajen gaisawa.

Mabiya addinin Hindu na amfani da wannan hanya wajen nuna girmamawa ko gaisuwa.

Tun bullar cutar Coronavirus, wasu wadanda ba mabiyan addinin Hindu ba ne, sun dauki wannan salon wajen gaisawa don kauracewa yin musabaha.

Jaridar Times of Israel ta ruwaito Firayim minista Benjamin Netanyahu yana ba 'yan kasarsa shawarar amfani da gaisuwar 'namaste' don kare kai daga kamuwa da Coronavirus.

Asalin hoton, Olivier Fitoussi/The_Times_of_Israel

Bayanan hoto,

Benjamin Netanyahu yana gaisawa da ministan lafiya na Isra'ila da salon gaisuwa na 'Namaste'

Wata jakadiyar Isra'ila a Indiya, Maya Kadosh ta wallafa sako a shafinta na Twitter inda ta ce tana godiya ga Indiya da ta samar da wannan salon gaisuwa, kuma daga yau 'yan Isra'ila sun samu salon gaisuwa.

Bullar cutar ta sa fargaba a zukatun mutane tun da har ta kai ana gudun gamuwa da juna ko taba juna kuma gwamnatoci da hukumomi sun soke manyan taruka masu muhimmanci saboda gudun yaduwar cutar.

Kasashe kamar Faransa da Japan sun soke duk wasu taruka da mutane fiye da 5000 za su taru a wuri guda, sai dai har yanzu babu wani bayani kan gasar wasanni ta Olympics da za a yi a Tokyo da za a fara a cikin wata Yulin bana.

A Burtaniya, hukumomi sun umarci asibitoci da su duba marasa lafiya ta hanyar kiran waya na bidiyo don rage barazanar yaduwar cutar.