'Yan bindiga sun kai hari a kasuwa a Zamfara

Zamfara Attack

Asalin hoton, Getty Images

Wasu da ake zargin `yan bindiga ne sun tarwatsa wata kasuwar kauye lokacin da take tsaka da ci a garin Dan Sadau na karamar hukumar Maru a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Wannan lamarin ya faru ne kwana guda bayan wasu 'yan bindigar sun far wa wani kauye inda suka kashe wasu mata biyu da namiji daya a kan hanyarsu ta kai wata amarya gidanta.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa maharan sun shiga kasuwar ne da tsakar rana akan babura kuma sun kai su "15."

SP Muhammad Shehu, kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce zuwan jami'ansu ne ya hana 'yan bindigar yin son ransu.

Kasuwar Mutunji dai ita ce kusan ta hudu a kauyen Dan Sadau da ake sayar da kayan lambu da dabbobi da sauran hajojin bukatun dan Adam.

Hakazalika kasuwar ta jima a rufe saboda tashe-tashen hankulan da suka addabi yankin, sai gashi cikin abin da ya yi kasa da wata biyu da bude ta, ta fuskanci wannan hari.

Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa maharan na shigowa kasuwar suka fara harbi.

"Sun karbe kudi da baburan mutane, sannan suka je shiga shagon wani mai sayar da lemo da ruwan sanyi suka kwashi kayan, suka wuce," a cewarsa.

Mutumin ya bayyana cewa maharan ba su wuce minti 20 ba a kasuwar suka fice a kan baburan.

Jihar Zamfara dai ta shafe shekaru tana fama da matsalar tsaron 'yan bindiga da barayin daji da masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.