Coronavirus: Saudiyya ta dakatar da mazauna kasar daga yin Umrah

Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Saudiyya ta sanar da dakatar da mazauna kasar daga yin aikin Umrah na wucin gadi a kokarin kasar na hana yaduwar Coronavirus.

Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar ta fitar wacce kamfanin dillancin labaran Saudiyyar SPA, ya wallafa a shafinsa na intanet, ta ce an dauki wannan matakin ne domin bayar da hadin kai ga hukumomin lafiya na duniya don shawo kan cutar.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Cikin Gidan ya danganta daukar matakin da kaguwar gwamnatin Saudiyyan na goyon bayan kokarin da duniya ke yi, musamman ma manyan hukumomi irin Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, na hana yaduwar cutar.

Amma sanarwar da aka fitar a ranar Laraba ta ce dakatarwar yin Umrar ta dan lokaci ce, kuma hukumomi za su ci gaba da nazari sannan za su janye matakin da zarar dalilan dakatarwar sun kau.

Sanarwar ta ce: ''Matakin dakatar da aikin Umrah ga mazauna kasar kari ne kan matakin gwamnati na dakatar da shigar baki masu ibadah Makkah da ziyara zuwa Masallacin Annabi a Madina, da kuma dakatar da shigar masu yawon bude ido daga kasashen da Coronavirus ta fi muni.''

Kazalika mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Cikin Gidan ya kara da cewa daukar matakin ya zama wajibi ne saboda a takaita yaduwar annobar daga shiga manyan masallatan biyu masu tsarki, wadanda miliyoyin mutane ke shigar su.

A ranar Litinin 2 ga watan Maris ne Saudiyya ta tabbatar da samun bullar cutar Coronavirus a karon farko a kasar a jikin wani dan kasar da ya koma kasar daga Iran.

A hannu guda kuma, Ministan Lafiya na kasar Dr. Tawfiq bin Fawzan Al-Rabiah, ya tabbatar da cewa sakamakon gwajin da aka yi mutum 51 da suka yi cudanya da mai dauke da cutar ya nuna cewa ba sa dauke da ita.

Asalin hoton, Masjid Haram Facebook

Sai dai ya ce ma'aikatarsa ta lafiya tana jiran sakamakon gwajin sauran mutum 19 din.

Matakan da ake dauka a Masallacin Harami

Tun bayan bullar cutar a kasar Saudiyya dai an ga yadda hukumomi ke ta kokarin daukar matakan da suka dace a Masallatan biyu, da suka hada samar da man goge hannu a kowace kusurwa da kuma kara yawan lokutan goge masallatan.

Sannan an ga yadda jama'a ke amfani da takunkumi don rufe hancinsu da bakinsu.

A kasa wasu hotuna ne na shugaban Masallatan Shaikh Abdurrahman Sudais yana tatsar abin goge hannun.

Hana Umra a mahangar addini

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A duk lokacin da aka ce an sa wata doka da za ta hana aiwatar da wata ibada musamman a masallatai masu tsarki, hankalin al'ummar Musualman duniya kan tashi, su fara tunanin ko hakan wani nakasu ne babba.

Wannan dalili ne ya sa Halima Umar Saleh ta tuntubi wani babban malamin Islama a Najeriya Dr. Mansur Yalwa, kuma malami a tsangayar koyar da aikin shari'a a Jami'ar Bayero da ke Kano kan yadda yake kallon wannan mataki na hana yin Umra gaba daya.

Dr Yalwa ya ce matakin abin a yaba ne sosai, don ya yi daidai da shari'ar Musulunci. ''Ita Shari'ar Musulunci dama an gina ta ne a kan manya-manyan ka'idoji guda biyu na jawo amfani da kuma hana barna.

''Duk abin da ake ganin zai iya jawo barna sai a tare shi tun kafin ya auku, idan kuma ya auku sai a yi kokari a rage yaduwarsa. Wadannan su ne abubuwan da aka gina Shari'ar Musulunci a kansu,'' in ji Malamin.

Da aka tambayi malam ko me yake gani idan aka ce an wayi gari babu wani mutum da ke dawafi a Dakin Ka'aba? Sai ya ce wannan magana ce ta mutane.

''Amma ai kaddarar Allah kala biyu ce akwai Kauniyya da Shar'iyya.

''Shar'iyya ita ce duk abin da ke da alaka da a bauta masa a yi masa aiki, Ya yi umarni da kaza ya hana kaza. Kauniyya kuma ita ce mai alaka da rayuwa wadda ba ta da alaka da umarni da hani sai dai abin da aka kaddara zai samu mutum mai kyau ko maras kyau.

''To Shar'iyya ita ce ta nuna cewa a bauta wa Allah a Dakin Ka'aba, to amma kaddararSa kuma Kauniyya tana iya sa ya zama wannan damar da aka samu ta zama an samu tsaiko a kanta.

''Don haka idan aka samu sabani tsakanin kaddara Shar'iyya da Kauniyya, to Kauniyyar ake dorawa a sama.

''Tun da ita za ta iya jawo wa mutane barnar da na fada dazu. Misali Annabi SAW ya ce 'Ka da a kawo marar lafiya a hada shi da mai lafiya.' Kun ga wannan mataki ne na kokarin kariya,'' in ji Malam.

Asalin hoton, Masjid Haram Facebook

Wasu da dama na nuna fargabar cewa wannan lamari na iya janyowa a kasa samun damar yin Umrar azumi ko kuma ma Aikin Hajji gaba daya a bana.

Sai dai masana sun ce ko da hakan ta kasance to ba abin fargaba ba ne ga al'ummar Musulmai don kuwa akwai lokacin da ba a yi aikin Hajji ba ma a tarihin Musulunci.

Dr Yalwa ya ci gaba da cewa: ''A shekaru ko karnuka na baya akwai lokacin da ba a yi aikin Hajji ba saboda yake-yake ko wasu dalilai. Ko Annabi SAW da kansa akwai lokacin da ya shirya zai je aikin Hajji sai aka hana shi shiga wanda wannan ne ya sa aka yi Sulhun Hudaibiyya, kuma ya hakura bai shiga ba.

''Saboda haka dalili yana iya sakawa a dakatar duk da dai ba haka aka so ba, amma saboda kokarin tsare al'umma kar wannan cutar ta yadu a can, to mu ma muna tare da wannan fatawar.

Malam Mansur ya ce yana da yakinin cewa tun da fari kasar Saudiyya ba ta dauki wannan mataki ba sai da ta tuntubi Majalisar Malamanta, ''duk da dai ban ga wata fatawarsu da suka fitar akai ba amma na tabbata lamari irin wannan sai an tuntube su.

Amfanin da Saudiyya ke samu daga ayyukan ibada

Wannan mataki da Saudiyya ta dauka na nufin ala tilas aka dauke shi idan aka duba irin asarar da ita kanta za ta yi.

Kowa ya san yadda kasar ke cin moriyar shigar baki masu zuwa ibada a addinance, da kuma a siyasance da zamantakewa da kuma ta fannin tattalin arziki.

''Haka kawai ba za ta hana zuwa aikin ibadar nan ba don kuwa za ta fi kowace kasa yin asara. Yanzu ga shi ta ce za ta mayar wa mutane kudadensu da suka biya, ai asara ce suka yi amma ba su da yadda za su yi.

''Ba ma fatan abin ya kai lokacin Umrar azumi amma idan har an kai ba yadda za a yi dole a hakura, tun da ai ita Umrar ba ta kai azumin kansa ba.

Duk abubuwa na Musulunci ana yinsu ne idan an samu dama, amma in ba a samu dama ba sai a hakura.

''Kuma daukar mataki na riga-kafi don kare yaduwar cuta ai Annabi SAW ne ya dora mu a kansa. Ya ce kar mai lafiya ya shiga garin da annoba ta fito kuma kar na ciki ya fita,'' a cewar Dr. Yalwa.