Shugaban Venezuela ya shawarci mata su yi ta hayayyafa don amfanin kasar

President of Venezuela Nicolas Maduro speaks during a press conference at Miraflores Palace on February 14, 2020 in Caracas, Venezuela

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya shawarci mata da su haifi yara shida-shida ''saboda ci gaban kasar."

Shugaban ya ba da shawarar ne a wani taro na gabatar da tsarin kiwon lafiyar mata da aka nuna shi a talabijin, inda ya cewa mata ''ku yi ta haihuwa, ku yi ta haihuwa.''

Kasar dai na fuskantar matsin tattalin arziki wanda ya jawo matsanancin karancin abinci da magunguna.

Tsakanin shekarar 2013 da 2018, kashi 13 cikin 100 na yaran Venezuela sun yi fama da tamowa, a cewar Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef.

Rikice-rikicen da aka yi ta samu tsakanin gwamnati da bangaren hamayya sun kara rikita halin da kasar ke ciki.

Kasashen duniya fiye da 50 suna daukar babban jagoran hamayya Juan Guaidó, a matsayin halastaccen shugaban kasar.

Amma Shugaba Maduro, jagoran masu tsattsauran ra'ayi wanda rundunar sojin kasar ke goyon baya, ya ki sauka daga mulki.

''Allah Ya yi miki albarka bisa haifar yara shida maza da mata da kika yi,'' a cewar Mista Maduro ga wata mata da ta halarci taron.

''Kowace mace ya kamata ta haifi yara shida saboda ci gaban kasar,'' a cewarsa, yana mai karawa da ''wannan makon mata ne'', da ke da alaka da Ranar Mata Ta Duniya da za a yi ranar 8 ga watan Maris.

Magoya bayan Mr Guaidó sun mayar da zazzafan martani a Twitter.

Manuela Bolivar, wata mamba a Majalisar Dokokin kasar da 'yan bangaren hamayya ke da rinjaye ta wallafa a Twitter cewa: ''Asibitoci ba sa cikin yanayi mai kyau, babu riga-kafi, mata ba sa iya shayarwa saboda yunwa kuma ba za su iya sayen madarar jararai ba saboda ta yi tsada, sannan kasar na fuskantar kaurar jama'a saboda mawuyacin hali da ake ciki.

''Maduro da duk mutanensa da suka fadi haka ba su da isasshen hankali.''

Wane hali iyalai suke ciki a Venezuela?

Duk mutum daya daga cikin 'yan Venezuelan uku na fama da yadda zai samu isasshen abinci mai gina jiki da zai ci, a cewar wani bincike da Hukumar Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi.

Ana tsaka da wannan hali na matsin tattalin arziki ne wata kungiyar agaji a 2018 ta ce yawan yaran da aka jefar a kan tituna ko aka bar su a mashigar wuraren da jama'a ke kai kawo ya karu da kashi 70 cikin 100.

Sai dai gwamnatin Venezuela ba ta bayyana wani adadi a hukumance ba a shekarun baya-bayan nan.