'Yan sanda 3 sun mutu a harin Damboa

Hari a Damboa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Majiyoyin soja sun ce 'yan bindigar sun gargadi mutanen garin kafin kai harin

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari a wani barikin soji da ke garin Damboa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Bayanai na cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar 'yan sandan kwantar da tarzoma uku sannan fararen hula kusan 19 sun jikkata.

Wasu kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa wata majiya a rundunar sojan Najeriyar ta ce 'yan bindigar sun rubuta wa mazauna yankin wasika cewar za su kai harin, wanda aka kai ranar Laraba.

Gwamnan jihar ta Borno, Babagana Umara Zulum ya yaba wa rundunar sojin bisa abin da ya kira "mahangurba ga Boko Haram" da sojojin suka yi wa kungiyar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar ranar Alhamis.

Ranar 3 ga watan Maris ne wasu masu ikirarin jihadi suka kai hari Bwalakila, wani kauye a karamar hukumar Chibok.

Haka kuma, a jihar Yobe mai makwabtaka 'yan bindiga sun kai hari garin Dapchi, inda kungiyar Boko Haram suka sace sama da dalibai mata 100 a wata makarantar sakandare a watan Fabarairun 2018.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kona gidajen mazauna garin da suka tsere.

Abu ne mai wuya a wasu lokutan a iya sanin hakikar wadanda suke kai irin wadannan hare-hare kasancewar ba Boko Haram ce kadai ke kai su ba.

Kungiyar Islamic State's West Africa Province (Iswap) ma tana kai hare-haren, wadda ta yi mubaya'a ga kungiyar IS.

A gefe guda kuma, rundunar sojan Najeriya ta saki mutum 223 daga kurkukunta a Maiduguri, bayan ta wanke su daga zargin alaka da kungiyoyin masu ikirarin jihadi.