Coronavirus ka iya shafar kasafin kudin Najeriya – Ministar Kudi

Zainab Shamsuna Ahmed

Asalin hoton, @ZShamsuna

Bayanan hoto,

Ministar ta ce coronvirus na yi wa farashin mai barazana a kasuwar duniya

Ministar kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana cewa kasar na duba yiwuwar yi wa kasafin kudinta kwaskwarima sakamakon barazanar cutar coronavirus ke yi wa farashin man fetur a kasuwar duniya.

Ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ranar Laraba.

Ministar ta ce zuwa yanzu dai cutar ba ta shafi yanayin tattara kudin harajin Najeriya ba da kuma farashin gangar man fetur, wanda ke kasa da yadda suka kiyasta a kasafin kudin.

Masharhanta na ganin cewa wannan yana da alaka ne da yadda Najeriya ke dogara kacokam kan man fetur kuma idan har abin ya shafi kasafin kudin to zai shafi ayyukan more rayuwa da gwamnati ta shirya yi wa talakawa.

"Dama can muna da niyyar sake duba kasafin kudi tun lokacin da aka saka hannu kan dokar kasafin," in ji ministar.

Ta kara da cewa: "Abin da muke kokarin yi shi ne, idan mu ga kudaden haraji sun yi kasa sosai to dole ne mu yi wa kasafin kudi kwaskwarima ta hanyar rage shi.

"Yanzu haka muna hako ganga miliyan 2 ta danyen mai amma yakan kai 2.1 a wasu lokuta. Wannan ma wata garkuwa ce.

"Ba mu dauki wasu matakai ba a yanzu har sai mun samu lokacin da ya dace sannan mu yi gyara kan kasafin ta hanyar hadin gwiwa da majalisun tarayya."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Har wa yau, ministar ta koka game da yadda wasu manyan kantuna ba sa cazar kwastomominsu sabon harajin kayan masarufi na VAT, wanda aka kara daga kashi 5 zuwa kashi 7.5 cikin 100.

Gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari ta ce ta kara yawan harajin ne domin samun kudaden aiwatar da kasafin kudin shekarar 2020.

"Game da harajin VAT, mun samu labarin cewa wasu manyan kantuna ba sa cazar harajin kan wasu kayayyakin abinci," Minista Zainab Ahmed ta fada.

"Idan ka sayi nama wanda aka sarrafa to dole ne ka biya haraji, amma idan ka je kasuwa ka sayi danye ko tumatur ko garin kwaki to babu harjin da za ka biya."

Ta kara da cewa su ma manyan kantunan suna da tsarabe-tsarabe da suke yi wurin sarrafa naman da kuma ma'aikata da suke biya albashi, talakawa kuma ka iya shiga kasuwa su yi sayayya a inda ba sai sun biya haraji ba.

"Saboda haka dole su caji harajin VAT musamman ganin cewa suna sayen kayan ne daga inda mutane ke sayowa sannan su sarrafa shi, su saka shi cikin mazubi," in ji ministar.