Sabbin bayanai takwas kan cutar Coronavirus a Najeriya

Dr. Osagie Ehanire
Bayanan hoto,

Dr Ehinire ya ce an killace mutum uku da ake zargin sun kamu da cutar

Ministan lafiya a Najeriya , Dr. Osagie Ehanire ya yi taron manema labarai a Abuja domin yin karin bayani kan yadda cutar Corona take a cikin kasar.

Ga bayanan da ya gabatar kan cutar:

  • Mutum 21 aka gwada domin tabbatar da ko suna dauke da cutar Coronavirus ko kuma a'a, kuma mutanen a jihohi hudu suke - Lagos da Kano da Abuja da kuma Ogun.
  • Mutum daya ne aka tabbatar yana dauke da cutar kawo yanzu, kuma dan Italiya ne a Lagos.
  • An killace wasu mutum uku da ake zargin ko sun kamu da cutar Coronavirus a Lagos (gwaji ne zai tabbatar da haka).
  • An gano mutum 55 daga cikin fasinjoji 148 da ke jirgin saman Turkiya wanda ya dauko dan kasar Italiyar da ya shigo da cutar Coronavirus a Najeriya.
  • Mutum 61 ne suka yi mu'amala da dan Italiyan da ya shigo da cutar watau 21 daga Lagos da kuma 40 a jihar Ogun. Dukkansu suna cikin koshin lafiya kawo yanzu.
  • Babu shirin rufe makarantu da wuraren ibada.
  • Akwai dakunan gwaji guda biyar domin tantance cutar Coronavirus a Najeriya: biyu a Lagos, daya a Abuja da Edo da kuma Osun.
  • Ma'aikatar Lafiyan Najeriya na tattaunawa da rundunar sojin ruwa da jami'an kwastam domin tabbatar da iyokokin kasar na cikin yanayin da ya dace.

Labaran da za ku so ku karanta kan coronavirus: