Yadda cutar coronavirus ke yaduwa abin tsoro ne - WHO

Gwajin coronavirus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cutar coronavirus ta kashe mutum sama da 3,000

Hukumar lafiya ta duniya ta ce kusan mutum 100,000 ke dauke da cutar coronavirus a duniya.

Sama da mutum 3,000 suka mutu - yawancinsu a kasar China.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa yadda cutar ke yaduwa babban abin tsoro ne, inda ya yi kira ga takaita yaduwar cutar a matsayin abin da kasashen duniya ya kamata yanzu su fi ba fifiko.

Wasu alkalumman hukumomi da kungiyoyi da suka kunshi har da Kamfanonin dillacin labaru kamar su Reuters da AFP sun ce adadin wadanda suka kamu da cutar sun haura mutum 100,000.

Suna dogaro ne daga bayanan da suka tattara daga hukumomin lafiya na kasashen duniya da cutar ta bulla.

Kasashe na baya-baya nan da cutar ta bulla sun hada da Vatican da Servia da Slovakia da Peru da Togo.

Cutar kuma na ci gaba da kara bazuwa a kasashen Italiya da Faransa da Iran.

Faransa ta shiga sahun kasashen da suka rufe makarantu saboda cutar coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Wadanne ne alamomin cutar?

Da alama tana farawa ne daga zazzabi, sannan sai mutum ya soma tari.

Bayan mako guda, mutum zai rika fuskantar yankewar numfashi.

Don haka ya kamata mutum ya je asibiti idan ya fuskanci irin wadannan alamomi.