Saudiyya ta kama 'yan gidan sarauta uku

Crown Prince Mohammed bin Salman

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana kallon Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a matsayin wanda shi ne ainihin ke mulki a Saudiyya

Wasu manyan 'yan gidan sarautar Saudiyya uku sun shiga hannun hukumomin kasar, cikinsu har da kanin Sarkin kasar Salman.

Ba a bayyana dalilan kama su ba, amma wasu jaridun Amurka na cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salma ne ya bayar da umarnin daukar wannan matakin a kansu.

Biyu daga cikin yarimomin na da karfin fada a ji a daular ta Saudiyya.

A 2017 Yarima Mohammaed bin Saman ya taba bayar da umarnin a kama kuma a tsare wasu manyan attajirai da ministocin kasar da kuma wasu manyan 'yan gidan sarautar Saudiyyar a wani otel mai suna Ritz-Carlton da ke Riyadh.

Ana kallon Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a matsayin wanda shi ne ainihin ke mulki a Saudiyya, tun bayan da mahaifinsa ya nada shi yarima mai jiran gado a 2016.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mohammed bin Nayef (a dama) tare da Mohammed bin Salman (a hagu) a 2015

'Yan gidan sarautar uku sun shiga hannun jami'an tsaro ne tun safiyar jiya Jumma'a, kamar yadda jaridun New York Times da Wall Street Journal suka wallafa.

Sunayen wadanda ake tsare da su: Ahmed bin Abdulaziz - wanda kanin Sarki Salman ne, da tsohon yarima mai jiran gado Mohammed bin Nayef, da kuma dan uwansu Yarima Nawaf bin Nayef.

Mohammed bin Nayef ya taba rike mukamin ministan cikin gida kafin aka cire shi dag mukamin bayan da Yarima Mohammed bin Salman ya sa aka yi masa daurin talala a 2017.