Ginin bene ya rufta kan mutanen da aka killace saboda Coronavirus

Rescuers search for survivors in the rubble of a collapsed hotel in Quanzhou, in China's eastern Fujian province on 7 March 2020.

Asalin hoton, AFP

A kalla mutum 70 ne suka makale a cikin wani otel da ya ruguje a China.

Otel din dai an ware shi ne domin killace wadanda ake zargi sun kamu da cutar coronavirus.

Hukumomi a kasar sun bayyana cewa an samu nasarar fitar da mutum 35 daga otel din mai suna Xinjia wanda ke da hawa biyar.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda jami'an bayar da agajin gaggawa ke kai dauki a ginin da ke lardin Fujian.

Babu bayanai dangane da abin da ya jawo ginin otel din ya ruguje.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, EPA

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 agogon GMT.

Kafofin watsa labarai na China sun ruwaito cewa ana amfani da otel din wajen killace wadanda aka tabbatar sun yi mu'amula da masu dauke da coronavirus.

An bayyana cewa an bude otel din ne a 2018 kuma yana da dakunan kwana 80.

Wata mata ta shaida wa kafar watsa labarai ta Beijing cewa 'yan uwanta na cikin wadanda aka killace a otel din.

''Na kasa samun su, ba su daukar wayoyinsu,'' in ji ta.

''Nima an killace ni a wani otel din, na shiga damuwa matuka, ban san abin da zan yi ba. Suna cikin koshin lafiya, ana yi musu gwaji a kullum kuma sakamako na nuna cewa suna cikin koshin lafiya.''

Map

Zuwa ranar Juma'a, lardin Fujian na da mutum 296 da suka kamu da coronavirus. Akwai kuma kusan 10,819 da ake sa wa ido sakamakon sun yi mu'amula da masu dauke da cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa sama da mutum 101,000 a fadin duniya sun kamu da cutar ta COVID-19.

Sama da mutum 3,000 suka mutu akasari a lardin Hubei inda aka fara samun barakar cutar.