Abubuwan da suka faru a farkon watan Maris din 2020

  • Mustapha Musa Kaita
  • Multimedia Journalist

Kusan ko wane mako, mukan yi kokarin bitar wasu daga cikin manyan labarai da muka wallafa kuma suka yi fice. A wannan makon ma, mun zakulo wasu daga cikin labaran da muka wallafa a farkon watan Maris din 2020. Duba kasa domin karanta labaran.

'Yan bindiga sun kashe mutum 50 a Kaduna

A farkon wannan watan, an kashe a kalla mutum 50 a harin da 'yan bindiga suka kai kan wasu kauyuka a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Igabi, Zayyad Ibrahim, ya bayyana wa BBC cewa maharan su sama da 100 sun dirar wa garin Kerawa da wasu makwabtan kauyuka inda suka kashe mutane suka kuma kona gidaje da motoci.

Hukumomi sun tabbatar da kai hari a garin na Kerawa a karamar hukumar Igabi amma basu tabbatar da adadin mutanen da aka kashe ba.

Harin ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama.

Asalin hoton, AFP

'Yan sanda sun kwace iko da ofishin jam'iyyar APC

AA farkon wannan watan ne 'yan sanda a Najeriya suka kwace iko da hedikwatar jam'iyya mai mulki a kasar ta APC, inda suka girke jami'ansu da dama da kuma motoci domin hana shiga ofishin.

Matakin ya zo ne sa'oi kalilan bayan wani hukuncin kotu da ya dakatar da shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole.

Yan sanda sun fada wa BBC cewa an basu umarnin su hana kowa shiga komai mukaminsa.

Tsare ofishin baya rasa nasaba da rikicin shugabanci da jam'iyyar ta APC mai mulki ke fama dashi.

Ikirarin gano maganin cutar coronavirus a Najeriya

Asalin hoton, @CHIKWE_I

A farkon wannan wata ne Farfesa Maurice Iwu wanda tsohon Shugaban Hukumar zabe ne a kasar ya yi ikirarin gano maganin cutar ta numfashi, wadda ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya, inda kuma kasarsa Najeriya ta kasance cikin kasashen da cutar ta bulla.

Sai dai jim kadan bayan wannan ikirari, shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu ya yi watsi da ikirarin Mista Iwu inda ya ce babu yadda za a yi a gano maganin cutar da ba ta dade da bulla ba a duniya.

Ya ce sabuwar cuta ce kuma ba a taba sanin da ita ba ko a fannin lafiya, sai watanni biyu da suka gabata.

Hakazalika ya ce kafin a gane tasirin maganin dole sai an gwada kan marasa lafiya, wanda da yawansu a China suke.

Amurka za ta ba da tukwicin ₦2.5b kan Shekau

Asalin hoton, AFP

A wani bangaren kuma, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ce ta yi tayin tukuicin dala miliyan, bakwai kwatankwacin sama da naira biliyan biyu da rabi ga wanda ya ba da bayanin da zai taimaka wajen kama Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubukar Shekau.

Amurka da mahukunta a Najeriya sun dade suna neman Shekau ruwa a jallo.

Ba wannan ne karon farko da Amurka da mahukunta a Najeriya suke irin wannan tayin ba.

Kazalika sojojin Najeriyar sun sha ikirarin kashe Shekau, amma daga bisani sai ya bulla a wasu hotunan bidiyo yana karyata su.

Real Madrid ta doke Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

A fagen wasanni kuma, Real Madrid ta yi nasarar cin Barcelona 2-0 a wasan mako na 26 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Real ta ci kwallon ta hannun Vinicius Junior saura minti tara a tashi daga wasan na hamayya da ake kira El Clasico.

Daf da za a tashi ne Real ta saka Mariano Diaz, kuma yana shiga fili ya ci Barcelona kwallo ta biyu.

Da wannan sakamakon Real ta dare mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 56, ita kuwa Barcelona ta koma ta biyu da maki 55.

A wasan farko a gasar La Liga ta bana da suka hadu a Camp Nou ranar 18 ga watan Disamba, sun tashi 0-0.

Rabon da Real ta ci Barcelona 2-0 a Santiago Bernabeu tun 16 ga watan Agustan 2017 a Spanish Super Cup.