Dankwairo na nan raye 'bai mutu ba - jikokin Dankwairo

  • Awwal Ahmad Janyau
  • BBC Abuja
Bayanan sauti

Tawagar Dankwairo Alhaji Danjuma

Latsa alamar lasifika a hoton sama domin sauraren tawagar Dankwairo

Marigayi Alhaji Musa Dankwairo Maradun na cikin mawaka na dauri da suka yi fice a kasar Hausa, kuma ake martaba su a fadin duniya.

Ko da yake ya rasu a wajajen 1991, amma jikokin marigayin sun ce Dankwairo yana nan a raye.

Alhaji Muhammadu Danjuma wanda yanzu shi ne Dankawairo, wato Sarkin Wakar Sarkin Kayan Maradun kuma jika ga marigayi Alhaji Musa Dankwairo ya shaida wa BBC cewa "Dankwairo bai tafi ba yana nan."

"Dankwairo yana nan, tun da zuriyarsa tana nan kuma waka ba mu daina ba. Ba a cewa babu Dankwairo domin yana nan," inji shi.

Alhaji Danjuma Dankwairo wanda mahaifinsa shi ne Daudun Kidi Muhammdu, ya kuma ce ko bayan ya kau akwai wanda zai jagoranci wakar gidan Dankwairo.

Gidan Dankwairo

Gidan Dankwairo gidan waka ne na Sarakunan gargajiya da attajirai da manoma, kuma shi kansa marigayi Alhaji Musa Dankwairo ya gaji waka ne daga mahaifinsa.

Bayan rasuwar mahaifinsa, yayansa Aliyu Kurna ne ya fara jagorantar tawagar waka kafin Alhaji Musa Dankwairo ya karba.

Dankwairo na cikin mawakan gargajiya da suka yi fice a tsakanin al'ummar Hausawa, inda wakokinsa suka yi tasiri wajen habaka harshen Hausa.

Dankwairo ya taka muhimmiyar rawa a fagen ilimi inda ya dabaibaye nazarin adabi musamman na baka da har gobe ake ci gaba da nazarin wakokinsa a jami'o'in Najeriya har ma da kasashen ketare.

Yana da wahala a iya kayyade adadin wakokin gidan Dankwairo, duk da cewa an yi nazari sosai a fagen ilimi game da wakokinsa da kuma wadanda suka gaje shi.

Wasu na ganin hanya mafi sauki da mutum zai iya tuna Sardauna ita ce sauraren wakokin Dankwairo saboda yadda ya wake marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan arewa.

A bagire na waka Dakwairo basarake ne saboda matsayinsa na Sarkin makadan Sarkin Kayan Maradun.

Tsarin tawagar Dankwairo

Asalin hoton, Dandalin magabata

Bayanan hoto,

Marigayi Alhaji Musa Dankwairo

A tawagarsa, Dankwairo shi ne Sarki tare da sauran sarakunansa da ke taimaka masa kuma dukkaninsu 'ya'yansa ne da 'yan uwansa.

Daudun Kidi shi ke bi wa Dankwairo a matsayin mataimaki, sai kuma Marafan kidi, sarautar da marigayi Alhaji Sani ya taba rikewa daya daga cikin 'ya'yan Dankwairo da suka yi fice da ake kira "Zakin Murya."

Akwai kuma Ciroma da Wakilin Kidi da Shamaki, dukkaninsu kowa da matsayinsa a tawagar Dankwairo.

Mun rike darajar gidanmu

Tawagar Dankwairo a yanzu ta kunshi jikokin marigayi Alhaji Musa Dankwairo ne wadanda ba su yi zamani da kakansu ba.

Daga cikinsu akwai Zakin Murya wanda ya gaji mahaifinsa marigayi Alhaji Sani Marafan Kidi. Akwai kuma 'ya'yan Alhaji Garba Daudun kidi.

Kuma kamar yadda suka gaji waka haka kowannensu ya gaji Kotso abin kidin mahaifansu da suka yi amfani da shi.

"Kowa nan yana rike da kotson mahaifinsa da ya gada, kuma kowa yana gane nasa duk da cewa kamanninsu daya," inji Dankwairo Alhaji Danjuma.

Ya kuma ce duk da ana cikin wani lokaci amma har yanzu suna rike da dajarar gidansu, domin duk da suna noma amma kuma da kidin suka dogara.

Barazanar wakokin zamani

Ana ganin wakokin zamani sun shafe wakokin gargajiya, saboda yadda samari suka rungumi sabon adabi na wakokin soyayya da ake amfani da kayan zamani.

Amma Dankwairo na yanzu Alhaji Danjuma ya ce ba su da wata matsala da wakokin zamani. "Bangarensu daban namu kuma daban"

"Muna nan matsayinmu na makadan gargajiya na sarakuna da attajirai."

"Muna nan rike da martabarmu, kuma tana nan, har yanzu sarakuna duk wanda aka ce ga Dankwairo nan ya zo, za su tarbe mu hannu biyu, ba wani matsala."

"Ba mu fuskantar kalubale na zamani," inji Alhaji Danjuma.

Ya kara da cewa ba abin da suka fi so shi ne Allah ya kara daukaka sana'arsu ta waka da daraja kamar yadda iyayensu da kakanninsu suka yi fice.

Alhaji Danjuma ya ce a rana sukan rera waka tara, kuma sun yi sabbin wakoki da suka hada da na Sarkin Kano da Sarkin Daura da Sarkin Gombe, kuma duk lokacin da za a yi nadin Sarki ana gayyatarsu.

Kalubale

Duk da cewa jikokin Dankwairon na fatan yin fice kamar kakansu marigayi Alhaji Musa Dankwairo amma akwai kalubale ganin yadda abubuwa suka sauya a yanzu.

Dankwairo ya yi fice ne a wakokin fada da kuma attajirai, amma ba za a kwatanta sarautun dauri da halin da sarautun yanzu ke ciki ba, musamman yadda tasirinsu ya ragu.