Coronavirus: An killace mutum miliyan 16 a arewacin Italiya

Military and police in Milan prepare to lock down the city

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jami'an sojoji da na 'yan sanda na shirin killace birnin Milan

Firai ministan Italiya ya ce a kalla mutum miliyan 16 kasar za ta killace a yankin Lombardy ciki har da wasu larduna 14 daga yanzu zuwa farkon watan Afrilu.

Wannan gagarumin sauyin lamarin ya biyo bayan kokarin da kasar ke yi ne domin dakile bazuwar cutar nan ta coronavirus, wanda ya hada da rufe makarantu da wuraren shakatawa da wanda jama'a da dama kan taru.

Batun ya kai ga ahar an dakatar da dukkan bukukuwan aure da na binne matattu har sai bayan lokacin da hukumomin kasar suka diba.

Italiya ce kasar Turai da cutar ta fi yi wa illa, wadda a ranar Asabar ta bayyana tashin goron zabi na wadanda suka kamu da cutar.

Kuma sabbin matakan kariyar za su shafi birnin Milan wadda cibiyar kasuwanci ce da Venice wadda ta kasance wurin ziyara ga miliyoyin masu yawon bude idanu har ranar 3 ga watan Afrilu.

Yawan wadanda suka rasa rayukansu sun kai fiye da 230, inda jami'ai a kasar ke cewa mutum fiye da hamsin sun mutu cikin kwana guda kawai.

Yawan wadanda suke da kwayar cutar ya kai 5,883 daga 1,200 a ranar Asabar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane a bisa layin sayen kayan abinci a Milan bayan da aka bayyana matakin killace yankin

Matakan da gwamnatin Italiya ta sanar sun hada da hana shiga ko fita daga yankin arewacin kasar na Lombardy, yankin da mutum miliyan 10 ke zaune cikinsa. Milan shi ne babban birnin yankin.

Za a kuma aiwatar da wannan hanin kan wasu larduna 14 da suka hada da Venice da Parma da Modena wadanda akwai jimillar mutum miliyan 16 cikinsu.

Firai minista Conte ya ce lardunan da killacewar ta shafa su ne Modena, da Parma da Piacenza da Reggio Emilia da Rimini da kuma Urbino.

Sauran su ne Alessandria da Asti da Novara da Verbano Cusio Ossola da Vercelli da Padua da Treviso da kuma Venice.