Ranar Mata Ta Duniya: Shin wane hali mata ke ciki?

Ranar Mata Ta Duniya: Shin wane hali mata ke ciki?

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hira da Fatima Auwal Aliyu, wata matashiyar da ta yi fice a fannin fasahar sadarwa ta zamani

A duk ranar 8 ga watan Maris din kowace shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Mata ta Duniya wadda kasashe da dama ke murnar zagayowarta.

An kebe wannan ranar ce a matsayin ranar tunawa da mata domin nuna mutuntawa da godiya da kuma kauna ga matan saboda gudunmuwar da suke bayarwa ga ci gaban al'umominsu ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da ma siyasa.

Taken bikin na bana dai shi ne 'duniyar da ake da daidaito duniya ce da kowa zai iya cimma burinsa'.

Mata dai na fuskantar kalubale da dama a rayuwarsu, kama daga cin zarafi zuwa wariya da ake nuna musu musamman a kasashe masu tasowa.

A kan hakane aka kebe wannan rana domin wayar da kan matan sanin 'yancinsu, da kuma nuna musu cewa su ma za a iya damawa da su a fannoni da dama na rayuwa.

A shekarar 1975 ne aka fara gudanar da bikin wannan rana.

Dangane da wannan rana, BBC ta tattauna da Fatima Auwal Aliyu, matashiyar da ta yi fice a fannin fasahar sadarwa ta zamani, sannan kuma ta ke horar da mata ilimin kwamfuta da na fasahar kere-kere, domin su ma a dama da su a wannan zamani na fasahar sadarwa.

Dubban mata ne ke gudanar da tattaki a fadin duniya domin murnar zagayowar wannan rana.

Sai dai a kasashe kamar Turkiyya, tuni hukumomi suka haramta irin wannan tattakin, amma duk da haka, masu fafutuka sun ce sai sun gudanar da tattakin a birnin Santambul na kasar.