Batutuwa biyar da suke addabar mata a Najeriya

.

Asalin hoton, Getty Images

Wani binciken Majalisar Dinkin Duniya da aka wallafa a ranar Alhamis, ya nuna cewa kusan kashi 90 cikin 100 na mutanen duniya na nuna bambanci ga mata duk da shekarun da aka shafe na kokarin daidaita 'yancinsu.

Mata ne kashi 50 cikin 100 na yawan mutanen duniya.

A Najeriya, kashi 49 cikin 100 na 'yan kasar mata ne, sai dai har yanzu matan kasar ba su da cikakken 'yanci kamar na sauran wasu kasashe.

Ga wasu daga cikin abubuwan da suka bambanta mazan Najeriya da matan kasar.

1. Dokar zama dan kasa

Sashi na 26 sakin layi na biyu na kundin tsarin mulkin kasar ya bada dama ga duk wata mace da ke auren dan Najeriya dama ta zama 'yar kasa, amma kuma ba a bada dama ba maza 'yan kasar waje masu auren matan Najeriya su zama 'yan kasa ba.

Da dama na ganin hana mata 'yanci daidai da maza wata hanya ce ta nuna wariyar jinsi kuma ta saba wa yarjejeniyar hana nuna wariya ga mata ta duniya wato CEDAW.

Wasu da irin wannan dokar ta shafa suna yawan korafi kan dalilin da ya sa ake nuna musu wariya a kasarsu ta haihuwa.

2. Auren Wuri

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Najeriya na daga cikin kasashen da suka yi fice dangane da auren wuri a duniya. Ko a wani rahoto da Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya fitar ya nuna cewa a cikin mata 10 ana yi wa hudu auren wuri kafin su kai shekara 18.

Kundin tsarin mulki na Najeriya ya bayyana cewa ''duk macen da ta yi aure, za a dauke ta a matsayin cikakkiyar mace mai hankali.''

A bangaren arewacin kasar inda Musulmi suka fi yawa, wasu shugabannin al'ummarmu sun yi yunkurin kayyde mafi karancin shekaran da za a iya yi wa mace aure, don tabbatar da cewa ta mallaki hankalinta. To sai dai malamai da dama sun kalubalanci yunkurin, inda suka ce haka ya saba wa addini.

Malaman sun ce shari'ar musulunci ba ta kayyade shekarun aure ba, don haka iyaye ne suke da ikon yanke shawarar yaushe za su aurar da 'ya'yansu.

Wadanda ke goyon bayan kundin tsarin mulkin sun bayyana cewa shari'ar musulunci bata fito fili ta bayyana me ake nufi da shekarun auren mata ba idan ana batun aure.

A daidai lokacin da namiji ke kokarin neman ilimi, ita kuma mace na shan gwagwarmayar aure da kuma daina zuwa makaranta inda za ta dukufa wajen yin ayyukan gida.

Asalin hoton, Getty Images

3. Matan da mazansu suka mutu

A al'adance, ana daukar mata a matsayin mallakar mazajensu, a wasu al'adun, duk lokacin da namiji ya mutu, mace kan fada cikin wani hali na takura da muzgunawa daga dangi.

Idan mace ta mutu, ba a so a ga namiji yayi kuka a fili, domin ana ganin kamar ya nuna gazawa a matsayinsa na shugaba a gida.

A wasu sassan Najeriya, a duk lokacin da namiji ya mutu, matar ce za a fara zargi da hannu a mutuwar mijinta, wanda hakan zai sa ta yi wasu abubuwa da suka sabawa ka'ida wajen wanke kanta.

A wasu sassan kasar ma, har fyade wasu mazan daga dangin miji suke yi wa matan a lokacin takaba, inda kuma za ta aske kanta kuma ta rinka saka bakaken kaya.

4. Zaman gidan haya

Kama hayar gida ga mata da yawa a Najeriya wani babban aiki ne, domin kuwa masu gidajen suna hana su gidajen domin tunanin cewa babu inda za su samu kudaden da za su rinka biyansu a duk shekara kan lokaci.

Akwai kuma masu gidajen hayar da ke da akidar cewa bai kamata mata su rinka zaman kansu ba a gidajen haya ba tare da iyayensu ba.

Sai dai wadannan dokokin ba su shafi maza ba.

Wata ma'aikaciya a Najeriya Olufunmilola Ogungbile ta shaida wa BBC cewa kashi 99 cikin 100 na masu gidajen hayar da ta je wajensu sun hana ta gidan haya saboda bata da aure.

Ta bayyana cewa akasarinsu suna yawan ce wa mace sai dai ta zo da saurayinta ko kuma mijinta.

Domin gujewa irin wannan nuna bambanci, mata da yawa kan je da wasu mazan wajen masu gidajen haya a matsayin mazajensu don a ba su gida.

Asalin hoton, Getty Images

5. Tazarar haihuwa

Bincike ya nuna cewa bambancin 'yanci tsakanin maza da mata na daga cikin abubuwan da ke kawo kalubale ga tazarar haihuwa a Najeriya.

Kashi 13 cikin 100 ne kacal na mata da ke tsakanin shekarun 15 zuwa 19 ke amfani da tsarin tazarar haihuwa.

Mata da dama ba su da ikon fara tazarar haihuwa ba tare da izinin mazansu ba, su kuma mazan suna da karfin saka matansu su rinka shan magunguna na tazarar haihuwa ko da kuwa matan ba su so.