Monica Dongban-Mensem: Mai ba da hannu a titi ta zama Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya

Monica Dongban-Mensem

Asalin hoton, Monica Dongban-Mensem

Bayanan hoto,

Monica Dongban-Mensem ce mace ta biyu da ta rike mukamin

Mai Shari'a Bolna'an Monica Dongban-Mensem, mai bayar da hannu a titunan babban birnin Najeriya Abuja (bisa radin kai) ce ta zama Shugabar Kotun Daukaka Kara a Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mai Shari'a Monica a mukamin na rikon kwarya ne biyo bayan ritaya da Zainab Bulkachuwa ta yi.

Zainab Bulkachuwa ta shafe shekara 43 a harkokin shari'a, sannan ta shafe shekara shida a matayin shugabar kotun daukaka kara.

Wannan nadi yasa Justice Monica ta zama mace ta biyu da ta shugabanci Kotun Daukaka kara ta Najeriya.

A lokacin da ba ta aiki, Mai Shari'a Monica Dongban-Mensem kan je titi ta rika bayar da hannu a Abuja.

Monica Dongban-Mensem 'yar asalin Jihar Filato ce, kuma ita ce Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Inugu kafin yanzu.

Ta yi karatun digirinta na farko da na biyu a bangaren shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.

Tarihin Rayuwar Monica Dongban-Mensem a takaice:

 • An haifi Monica Bolna'an Dongban-Mensem ranar 13 ga watan Yunin 1957
 • A garin Dorok na Karamar Hukumar Shendam aka haife ta
 • Tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Kara reshen Jihar Inugu
 • Marubuciyar littafin The Defendant a shekarar 1991
 • A Jami'ar Ahmadu Bello Zaria ta yi digiri na farko da na biyu
 • Ta yi difiloma a cibiyar Advanced Legal Studies, ta Jami'ar London, Russel Square
 • Tsohuwar mai shari'a ce a kotun Abuja
 • Tsohuwar rijistira a Babbar Kotun Jihar Filato a shekarar 1979
 • Tsohuwar malama a cibiyar Catholic Media Centre da ke Kaduna
 • Tsohuwar malama a Jami'ar Jos
 • Ta kafa gidauniyar Pa William Mensem Education

Dalilin da ya sa take bayar da hannu a titi

Bayanan hoto,

A lokacin da ba ta aiki, Monica Dongban-Mensem kan je titi ta rika bayar da hannu a Abuja

A lokacin da ba ta aikin komai, Mai Shari'a Monica Dongban-Mensem kan je titi ta rika bayar da hannu a Abuja, shekara takwas bayan da wani ya kade danta da mota, ya mutu.

Idan ka gan ta za ka tabbatar lallai aikin ta fito yi da gaske, kamar yadda wakiliyar BBC ta sashen Pidgin ta ruwaito kwanakin baya da ta ci karo da ita tana kan aikin nata.

"Mafi yawancin 'yan Najeriya dai ba su da hakuri, kuma ana iya gani ma ko a tukinsu," in ji Monica.

'Yar kimanin shekara 62, Monica ta kafa wata kungiya da ta sanya wa sunan danta - Kwapda'as Road Safety Demand.

Ta yi hakan ne domin a rika horar da masu tuka mota a kan yadda za su rinka kiyayewa, sannan kuma tana shirin samar da makarantar koyon tuki ga direbobin motocin haya.

Bayanan hoto,

Monica Dongban-Mensem, a tsakiya a lokacin da ta karbi takardar shaidar kammala horon da ta samu na bayar da hannu

Ba a nan kawai ta tsaya ba, Justice Dongban-Mensem, na son ta rinka bayar da hannu da kanta.

Bayan ta shafe wasu makonni tana karbar horo a hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya, ta samu shaidar cewa za ta iya bayar da hannu a tituna.

A lokacin, shekara biyar da mutuwar danta, anan ta ziyarci wajen da aka kade danta a tsakiyar birnin Jos na jihar Filato.