Coronavirus: Farashin man fetur ya fadi 'warwas' a kasuwannin duniya

Mai

Asalin hoton, Getty Images

Farashin mai ya yi faduwar da bai taba yin irinsa ba a cikin shekaru, hakan kuma ya kara daga wa kasashen duniya hankali.

Kashi 30 cikin 100 na faduwar farashin ya faru ne saboda matakin Saudiyya na kara samar da mai, bayan Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur, OPEC, ta gaza cimma matsaya da Rasha kan kara wa'adin rage samar da man.

A halin yanzu dai akwai man da yawa a kasuwa, yayin da farashin ke faduwa saboda barkewar annobar coronavirus.

Kasuwar hannayen jari a Asiya ta fuskanci koma baya da fargaba a bangaren masu zuba jarin.

Matsayin mai na Brent ya ragu da dala 31.02 kan kowace ganga a ranar Litinin, a kasuwannin makamashi mai sauyawa.