Rikici ya barke a majalisar dokokin Kano kan Sarki Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano Sanusi na biyu

Rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ranar Litinin kan yunkurin da majalisar ke yi na "ladabtar" da Sarki Muhammadu Sanusi II.

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne bayan bukatar da mataimakin shugabar majalisar dokokin, Hamish Ibrahim Chidari, ya yi cewa a gabatar da rahoton da kwamitin da majalisar ta kafa domin binciken Sarki Sanusi II.

Ranar hudu ga watan Maris ne majalisar ta ce ta karbi korafe-korafe biyu da suka zargi Sarki Sanusi II da yin kalaman da basu dace da addinin Musulunci da al'ada ba.

Shugaban majalisar ya shaida wa 'yan majalisa cewa ya karbi korafe-korafen ne daga wata Kungiyar Bunkasa Ilimi da Al'ada ta Kano da kuma wani mutum, Muhammad Mukhtar mazaunin karamar hukumar Gwale.

Amma bai fayyace abubuwan da Sarki Sanusi II ya yi ba wadanda suka saba addini da al'adun Kano.

Daga nan ne shugaban majalisar ya bai wa kwamitin mako daya domin ya yi bincke sannan ya mika rahoton kan batun.

Kuma yunkurin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Dala, Lawal Usaini, ya yi na neman karin bayani kan korafin da shaidun da aka gabatarwa majalisar bai yi nasara ba saboda shugaban majalisar ya hau kujerer na-ki inda.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An kwace sandar majalisa

Amma a zaman majalisar na ranar Litinin, wasu 'yan majalisar musamman magoya bayan jam'iyyar PDP da kuma wasu na jam'iyyar APC sun ki amincewa a gabatar da rahoton kwamitin.

Sun yi zargin cewa magoya bayan APC na yunkurin tsige Sarki Sanusi II ba tare da wata hujja ba.

Amma 'yan majalisar na APC sun dage cewa sai sun yi wannan zama.

Rahotanni sun ce daga nan ne shugaban marasa rinjaye, Isyaku Ali Danja, ya yi kokarin dauke sandar majalisar lamarin da ya haifar da kokawa tsakanin mambobin majalisar.

Hotunan bidiyon da aka dauka a majalisar sun nuna yadda ake ta ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan majalisar inda daga bisani aka aka fita da sandar majalisar.

Wannan lamari dai na faruwa ne a yayin da mazauna jihar ta Kano ke ci gaba da fama da radadin talauci da rashin ababen more rayuwa.

Ko a makon jiya, wani malamin addinin Musulunci a jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya caccaki 'yan majalisar bisa kawar da kai wajen inganta rayuwar mazauna jihar inda suka mayar da hankali kan cire Sarki Sanusi II.

Ya bayyana su a matsayin matsorata wadanda suka kasa fitowa fili su aiwatar da manufarsu ta son cire sarkin, yana mai cewa bai kamata su rika mayar da batun kamar wasan kwaikwayo ba.

"Idan kuna son sarkin nan ku bar idan ba kwa sonsa ku cire shi," in ji Sheikh Daurawa, yana masi karawa da cewa bai kamata a rika wasa da hankalin al'ummar Kano ba.