Dalilai biyar da suka sa Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dalilan da suka sanya ta cire Sarki Muhammadu Sanusi II daga kan mulki.

Sarki Sanusi II

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Litinin ne wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya fitar ce ta bayyana dalilan cire sarkin.

Sanarwar ta ce daukacin mambobin majalisar zartarwar jihar sun amince a cire Sarki Sanusi II.

BBC ta ga dalilan da gwamnatin ta bayar, sannan ta tuntubi masana harkokin siyasa kan karin dalilan cire Sarkin:

Rashin Biyayya

Sarkin Kano yana nuna rashin biyayya ga umarnin ofishin gwamna da na sauran hukumomin gwamnati, ciki har da rashin halartar tarukan da gwamnati ke gayyatarsa ba tare da bayar da wata kwakkwarar hujja ba. ''Hakan rashin biyayya ne,'' in ji sanarwar gwamnatin.

A bayyane take cewa sau da dama Malam Muhammadu Sanusi II ya ki yin biyayya ga sashe na uku karamin kashe na 13 (a - e) na dokar Masarautar Jihar Kano ta shekarar 2019 kuma idan aka bar shi ya ci gaba da haka, zai bata mutuncin Masarautar Kano.

Kare Mutuncin Kano

Sanarwar ta kara da cewa an dauki matakin tube wa Sarki Sanisu II rawaninsa ne domin kare mutunci da al'ada da addini da kuma kimar Masarautar Kano wacce aka gina shekaru dubbai da suka gabata.

Sukar Manufofin Gwamnati

Mai sharhi a kan harkokin siyasa, Kabiru Sa'idu Sufi, Malam a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano, ya shaida wa BBC cewa babban dalilin cire Sarki Sanusi II daga kan mulki shi ne sukar da yake yi wa manufofin gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Wasu da dama na ganin sukar da sarkin ya yi wa shirin gwamnatin jihar na karbo bashi daga kasar China domin gina layin dogo a cikin birnin Kano na daga cikin dalilan da suka fara harzuka gwamnatin jihar.

A matsayinsa na masanin tattalin arziki, Sarkin na Kano ya ce babu wani alfanu da za a samu idan aka ciyo bashi domin aikin babu wata riba da Kano za ta samu da shi.

Wannan kalami ya fusata gwamnatin Kano, abin da ya sa aka fara takun-saka, kuma dangantaka ta fara yin tsami.

Lamarin ya kai ga yunkurin sauke Sarki daga sarauta da kuma kaddamar da bincike kan zargin kashe kudin masarauta ba bisa ka'ida ba.

Wasu manya da suka hada da mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Alhaji Aliko Dangote sun shiga tsakani domin sasanta gwamnan Kano da Sarkin Kano.

Sai dai Sarkin ya sha cewa an jujyawa maganganunsa.

Siyasa

Magoya bayan gwamnatin jihar Kano sun sha kokawa kan zargin da suke yi wa sarkin na shiga harkokin siyasa.

Gwamnan Kano da magoya bayansa sun zargi Sarki Sanusi da goyon bayan dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna.

Sun yi zargin cewa ya fito fili ya yaki Ganduje, kuma ya yi amfani da kudinsa wajen yi wa dan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP yakin neman zabe, sai dai sarkin ya musanta wannan zargi.

Wannan dalili ne yasa lokacin da Gwamna Ganduje ya ci zabe karo na biyu, magoya bayansa suka shiga wani babban dakin taro na gwamnatin jihar suka cire hoton Sarki Sanusi II.

Hakan ya janyo gagarumar baraka tsakanin shugabannin biyu, lamarin da ya kai ga gwamnatin na yunkurin tube sarkin.

Gididdiba masarautar Kano

Bayanan hoto,

Gwamna Abdullahi Ganduje ya gididdiba masarautar Kano zuwa gida biyar

Ana ganin kirkirar karin masarautu hudu a cikin Masarautar Kano a matsayin wata alama tun da fari ta sauke Sarki Sanusi.

Al'amarin ya yi matukar harzuka masarauta da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Masarautun da Gwamna Ganduje ya kirkira su ne: Gaya, Karaye, Bichi da kuma Rano.

Hakan ya sa masu nada sarki a Kano gurfanar da gwamnatin Ganduje a gaban kotu lamarin da ya sake rura rikicin da ke tsakanin Sarki Sanusi II da Gwamna Ganduje.

Wane ne Sarki Muhammadu Sanusi II?

Asalin hoton, Getty Images

  • An haifer shi a gidan Sarautar Fulani, kuma Lamido Sanusi ya zama Gwamman Babban Bankin Najeriya a 2009
  • Gwamnatin Goodluck Jonathan ta cire shi daga aiki a 2014 bayan ya yi zargin cewa ribar da aka samu ta $20bn daga man fetur ta salwanta
  • Mujallar TIME ta ayyana shi a jerin mutane masu karfin fada-a-ji a 2011
  • A 2013, Gidauniyar the Global Islamic Finance Awards ta ba shi lambar yabo kan bunkasa harkokin bankin Musdulunci a Najeriya
  • An nada shi Sarkin Kano na 14 a 2014 kuma kakansa shi ne sarkin Kano na 11
  • An cire shi daga mulki ranar tara ga watan Maris na 2020