Waye zai zama sabon Sarkin Kano?

.

Tun bayan bayyana sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a yanzu hankula sun karkata zuwa wanda zai zama sabon sarkin Kano.

A doka dai zuri'ar gidan Dabo ne kawai za su iya sarautar Kano. To sai dai zuri'ar tana da yawa kuma ta kasu gida-gida.

Kawo yanzu dai gwamnatin ba ta bayyana lokacin da za a nada sabon sarki ba. sai dai ana sa ran cikin kwanaki masu zuwa za a bayyana sabon sarkin.

Sai dai hankula sun fi karkata ne zuwa gidajen Sarki Muhammadu Sanusi I da kuma gidan Ado Bayero.

Galadiman Kano Abbas Sanusi (Gidan Sarki Sanusi)

Galadiman Kano dan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ne, kuma yana daga wandanda suka fi dadewa da mukami a fadar kano.

Dansa Abdullahi Abbas shi ne shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Kano, kuma yana da karfin fada a ji a gwamantin Kano. Mai yiwuwa ya yi tasiri wajen ganin an bai wa mahaifinsa sarautar wanda an tabbatar ya jima yana nema.

Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero (Gidan Ado Bayero)

Mutane da dama musamman na kusa da gwamnati sun jima suna daukar Aminu Ado Bayero a matsayin wanda za a bai wa sarautar Kano da zarar an sauke Sarki Sanusi.

Tun shekarar 2017 aka fara takaddama tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi. Aminu Ado yana da farin jini a wajen mutanen Kano, don haka gwamnatin za ta iya nada shi don ya gaji mahaifinsa Ado Bayero, wanda har yanzu jama'ar Kano suke mutuntawa.

Ciroman Kano Nasiru Ado Bayero (Gidan Ado Bayero)

Wani wanda ake yi wa fatan zama sarkin kuma zai iya kasancewa zabin gwamnati shi ne Ciroman Kano Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Duk da yake a shekaru Aminu Ado gaba yake da shi, yana da matukar tasiri cikin 'ya'yan Ado Bayero saboda kusancinsa da mahaifinsu a lokacin da ya ke raye.

Kuma mutane da dama na ganin ya cancanta ya zama sarkin Kano saboda halayyarsa irin ta sarakuna ce.